Wani abun da ya sa 'yan Najeriya suka fi son Hillary Clinton ita ce barazanar da Donald Trump yayi na cewa zai hana baki shiga kasar musamman musulmai.
Wasu mazauna jihohin Adamawa da Taraba sun bayyana fatansu ga sabuwar ko sabon shugaban Amurka da zaben jiya zai fitar. Suna fatan ko mace ce ko namiji ne ya zama shugaban Amurka, to ta dauki matakai ko ya dauki matakan da zasu kawo zaman lafiya a duniya. Suna mai cewa fitinu sun yi yawa a duniya kamata yayi a ragesu.
Irin kasar Najeriya da ta sha fama da rigingimu sun kira a taimaka mata domin mutane su koma rayuwa cikin lumana da walwala. A arewa maso gabas, misali, akwai talauci da rashin ilimi da dai sauransu. Suna son tsayawa kasar yadda za'a samu kudi a sake gina arewa maso gabas.
Muhammad Awal mazauni a Yola yayi fatan kowa ya hau ya tabbatar da zaman lafiya a duniya domin yanzu duk inda ake tashin hankali, injishi, akwai hannun Amurka a ciki. Yayi fatan Allah ya ba kasar shugabancin da zai nemi sulhu da cigaba.
Onarebul Hindi cewa yayi muddin Hillary Clinton ta ci zabe zata cigaba da manufofin Shugaba Barack Obama tare da yiwa wasu kasashe taimako.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.