Masu nazarin suka ce a Afirka zabuka sukan kare da tashin hankali da yamutsi da salwantan rayuka saboda yin watsi da sakamakon.
Zabuka a Afirka sukan jawo dauki ba dadi da murdiya da magudi da dai wasu halaye da basu dace ba.
Wani Malam Musbau Alkadiri ya kara da cewa kasashen Turai sun fi 'yan siyasan Afirka iya siyasa da iya mulki. Yace a tarihin Amurka ba'a bata fitowa a ce an yiwa wani magudin zabe ba. Yadda turawa suka kawowa kasashen Afirka siyasa ba haka 'yan Afirka suke yinta ba.
Su kuma masu goyon bayan 'yan takaran suna cigaba da bayyana ra'ayinsu. Sun bayyana alfanu zaben Hillary Clinton ko Donald Trump.
Malam Kura Bilyaminu yace Hillary Clinton tana da manufa mai dama dama bisa ga Donald Trump. Tana da manufar hada kan amurkawa da hada kawunan kasashen dake da hulda da Amurka.
Masu goyon bayan Donald Trump suna shakku akan wasu matakai da yace zai dauka da zara an zabeshi. Malam Aliyu yace wasu maganganun sa sun kawo cecekuce masu tsanani cikin kasar ta Amurka. Trump yayi barazana da yawa kamar hana musulmi shiga Amurka. Haka shi Trump yace bai yadda da wasu yarjeniyoyi da kasar ta cimma ba.
Ga rahoton Mamman Haruna da karin bayani.