Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Cigaba da Bayyana Sakamakon Zaben Amurka da Aka Yi Jiya


'Yan takaran shugabancin Amurka
'Yan takaran shugabancin Amurka

Har yanzu ana ci gaba da karban sakamakon zaben shugaban kasa na Amurka da aka yi jiya na wannan shekara ta 2016, kuma izuwa yanzu ‘yan takaran, Hilary Clinton ta Democrats da Donald Trump duk suna ci gaba da lashe jihohin da aka yi zaton zasu lashe.

Sai dai har yanzu ana zaman dar-dar kan yadda sakamakon manyan jihohi irinsu Pennsylvania, Michigan, da New Hampshire zasu kasance, da yake suna kusan kut da kut a yawan kuri’un da kowannensu ya samu.

Dan takara dai yana bukatar samu kuri’un mazabu 270 kafin shi ko ita su iya lashe zaben shugaban kasa.

Hilary Clinton da mijinta tsohon shugaban Amurka Bill Clinton sun jefa kuri’ansu a birnin New York ne kuma a nan suke zaune yanzu haka suna jiran ganin yadda daren zai kare da sakamakon da zai bulla.

Shima Donald Trump na jam’iyyar Republican yana nan cikin makeken gidansa mai soraye dake New York, yana jiran ganin yadda al’amarin zai kasance.

XS
SM
MD
LG