A yau Laraba, a sanarwar da ta wallafa a shafinta na Telegram, kungiyar Hezbollah ta sha alwashin ci gaba da gwagwarmayar tallafawa al’ummar Gaza sannan ta yi alkawarin daukar fansa a kan harin na jiya Talata.
Asibitin Awda, inda aka kai gawawwakin, ya tabbatar da adadin wadanda suka mutun sannan yace an raunata mutane 13. Bayanan asibitin su nuna cewa wadanda suka mutun sun hada da wata uwa da jaririnta da kuma ‘yan uwanta 5.
Wasu fitattun malaman addinin Islama daga Najeriya sun yi kira ga 'yan Afrika mazauna Turai da suka fito kwansu da kwarkwatarsu domin sauraran wa’azi daga bakin maluman a taron da aka saba gudanarwa shekara-shekara a Turai a kan muhimmancin zamantakewa mai kyau.
A kudu maso yammacin Poland, ruwa ya ci mutum daya an kuma sauya wa dubban mutane matsugunni a tsallaken iyaka a Jamhuriyar Czech, yayin da ruwan sama kamar da bakin kwarya ke ci gaba da sauka a tsakiyar nahiyar Turai a yau Lahadi, lamarin da ya haddasa ambaliyar ruwa a wurare da yawa.
Kasashen duniya na ci gaba da fadi tashin ganin an samu mafita a rikicin Gabas Ta Tsakiya ta wajen daukar matakin da zai dan gamshi kusan kowa, kuma kowa zai hakura da abin da ya samu.
An yankewa, Tyrese Haspil, hukuncin zaman gidan kaso na shekaru 40 zuwa daurin rai-da-rai a shari’ar kisan kai da sare kan shugaban wani kamfanin fasaha, Fahim Saleh, da ta gudana a yankin Lower Eastside a shekarar 2020.
WHO ta wallafa a shafinta na X a yau juma’a cewa, ana sa ran samun alluran rigakafin ya hanzarta yakin da ake yi da annobar dake bazuwa a nahiyar Afirka.
Thomas- Greenfield ta shaida wa Kwamitin Hulda da kasashen Wajen cewa “Shekara da shekaru, kasashen nahiyar suna ta kiraye-kiraye a samar da wata majalisa mai kunshe da wakilai, wacce za ta nuna kowane yanki na duniya
Blinken ya ce harin zai sak mayar da hannun agogo baya a yunkurin da ake yi na ganin an kulla yarjejeniyar dakatar da bude wuta.
A cikin bidiyon da jaridar UK Mirror ta ruwaito an ga dan sandan yana magana cikin harshen Yarbanci, daya daga cikin manyan harsunan da ake amfani da su a Najeriya
Hare-haren da Isira'ila ta kai sun kashe a kalla mutane 34, ciki har da mata da kananan yara 19.
Domin Kari
No media source currently available
Bilkisu Nana Hassan, wata ma’aikaciyar gwamnati da ta yi ritaya a Kaduna, ta ce mata za su iya rungumar yin noma na zamani a cikin gidajensu, ba tare da sun je ko ina ba.