Mai magana da yawun fadar White House a fannin tsaro, John Kirby ya shaidawa gidan talabijin din CNN cewa "galibin makaman da aka harba ta sama, daga Iran aka harba su.
Jiragen Iran marasa matuka sun nufi Isra'ila, in ji Press TV na kasar Iran mai yada labarai da harshen Ingilishi, yayin da ya ambato majiyoyin Iran.
Jiragen saman Isra'ila sun kashe 'ya'yan babban jagoran siyasar Hamas guda uku a zirin Gaza a jiya Laraba, a daidai lokacin da Isra'ila ke gudanar da tattaunawar tsagaita bude wuta da kungiyar ta Hamas.
Ministan harkokin cikin gida na kasar Turkiyya ya ce ‘yan sanda sun kama hodar ibilis mafi girma na uku a tarihin kasar.
Kasar Sin ta sanar da sanya takunkumai da ba kasafai aka saba gani ba a kan wasu kamfanonin tsaron Amurka biyu, saboda abin da ta ce na goyon bayan sayar wa Taiwan makamai.
Mutane 9 da suka hada da jariri daya ne suka mutu bayan kifewar kwale-kwalen da suke cikin a lokacin da suke kokarin tsallakawa tekun Bahar Rum a cikin yanayi mai hadari, kuma ana fargabar bacewar wasu mtuane 15, kamar yadda ma’aikatan tsaron gabar ruwan Italiya suka sanar a yau Alhamis.
A yau Alhamis, sojojin Isira’ila sun sanar da abin da suka kira, sababbi matakai da aka inganta na shigar da kayan agaji zuwa zirin Gaza, cikin har da gina wata sabuwar mashiga ta kasa a arewacin Gaza.
A ranar Lahadin da ta gabata ne dan tsere Russ Cook ya isa yankin arewacin Afirka, kusan shekara guda bayan ya tashi daga kudancin nahiyar a yunkurinsa na kure tsawon nahiyar da gudu.
Al’ummar Musulmi a sassan duniya sun gudanar da bukukuwan Sallar Idi yau Laraba, inda aka kammala azumin watan Ramadan tare da saduwa da ‘yan uwa da kuma sa sabbin tufafi da cin kayan kwalama.
Ministan harkokin wajen Isra'ila ya yi barazana a yau Laraba cewa, sojojin kasarsa za su kai farmaki kan Iran kai tsaye idan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kai hari daga yankinta kan Isra'ila.
Fadar Vatican ta ayyana cewa aikin tiyatar canza jinsi da na dakon cikin wasu da mata ke yi a matsayin babban cin mutuncin bil adama, inda ta sanya su a matsayi daya da zubar da ciki da kuma kisan kai a kuma matsayin ayyukan da suka yi watsi da shirin da Allah ya tanada a rayuwar ‘dan adam.
Wani jami'in Hamas ya ce a ranar Litinin din nan ba a samu wani ci gaba ba a sabon zama na shawarwarin tsagaita wuta a Gaza a birnin Cairo, taron da kuma ya samu halartar tawagogin Isra'ila, Qatar da kuma Amurka, jim kadan bayan da majiyoyin Masar suka ce an cimma matsaya kan ajandar da aka daukaka
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.