WASHINGTON, D. C. - Ofishin kula da koyarwar addini na Fadar Vatican ya fitar da wani bayani mai shafuka 20 na bayanan matsayin darikar da aka dauki biyar ana nazari a kai. Bayan gagarumin bita a cikin 'yan watannin nan, Paparoma Francis ya amince da shi a ranar 25 ga Maris, wanda ya ba da umarnin buga wa.
A cikin wani sashe da ake ta dako, Vatican ta sake yin watsi da ka'idar jinsi, ko ra'ayin cewa ana iya canza jinsin mutum. Fadar ta Vatican ta ce Allah ya halicci namiji da mace da jinsi daban-daban a ilimin halitta, halittu daban-daban, kuma ya ce kada mutane su yi la'akari da neman canja wannan shirin ko kuma su yi kokarin maida kan su "Allah."
"Ya biyo baya da cewa duk wani canja jinsi, yana yin barazana ga mutunci na musamman da mutum ya samu tun lokacin da aka yi ciki," in ji takardar.
Ya bambanta tsakanin tiyata da ke tabbatar da jinsi, wa aka haramta, da kuma "rauni na al'aura" da ke faruwa a lokacin haihuwa ko kuma wanda ke tasowa daga baya. Ana iya "daidaita" wadannan abubuwan da rashin daidaituwa tare da taimakon kwararrun likitocin kiwon lafiya, in ji shi
Masu fafutukar kare hakkin Katolika na LGBTQ+ nan da nan suka soki takardar da cewa bata ta fiya da zamani, mai cutarwa kuma ta saba wa manufar da aka bayyana na sanin daraja mara iyaka na duka mutanen da Allah ya halitta. Sun yi gargadin cewa zai iya yin tasirin gaske a kan mutanen da abin ya shafa, yana kuma iya haifar da tashin hankali da nuna wariya.
Dandalin Mu Tattauna