Jami'an 'yan sanda sun tsaya kusa da sakateriyar gwamnatin tarayya a Abuja, domin kula da kara tabbatar da tsaro.
Hotunan 'yan gudun hijirar Najeriya wadanda aka maido daga kasar Kamaru a lokacin da suka isa sansanin 'yan gudun hijira da yake Furore a Yola da Sojojin dake binciken su.
Tsohon Sakataren Harkokin Wajen Britaniya David Milliband Ya Ziyarci 'Yan Gudun Hijira A Yola.
Shugaban Kasar Tanzania John Magufuli ya jagoranci wani aikin tsaftacen kasar a bikin tunawa da ranar samun 'yancin kai karo na 54, jami'an Gwamnati da tsohon shugaban kasa Jakaya Kikwete suma sun fito sun hadu da jama'ar gari wajen tsabtace muhalinsu.
Hukumomi a San Bernardino a California sun gano wadanda ake zargi da harbin kan mai uwa da wabi da yayi sanadiyar mutuwar mutane 14, da jirkita mutane17.
Nnamdi Kanu ‘dan gwagwarmayar tabbatar da ware yankin Biafra a matsayin kasa daga Najeriya, wanda ya zauns rabi a Najeriya rabi a Ingila, an kamashi kan laifin zama shugaban haramtacciyar kungiya, za kuma a gurfanar da shi gaban kuliya a Abuja.
Kowace Ranar 1 Ga Watan Disamba Rana Ce Da Hukumar Lafiya Ta Duniya Ta Tsayar Domin Tunawa Da Masu Cutar Kanjamau A Fadin Duniya, Disamba 1, 2015.
Shugabannin Kasashen Duniya Sun Hadu Domin Zantawa Akan Kare Matsalolin Dumamar Yanayi Da Ke Ma Duniya Barazana A Birnin Bourget Kusa Da Paris Na Kasar Faransa, Nuwamba 30, 2015.
Fafaroma Ya Yi Maganganu Na Dama A Taron Da Aka Gudanar A Nairobi Kangemi Kasar Kenya
Hotunan kaddamar da yaki da zazzabin cizon sauro a jihar Kaduna, Nuwamba 26, 2015
Domin Kari