Kasar Chadi ta ba da sanarwar kawo karshen yarjejeniyar ayyukan sojan da ta sabunta da Faransa a shekarar 2019. Gwamnatin Chadin ta ce ta dauki wannan matakin ne da nufin jaddada ‘yancin kanta shekaru 66 bayan samun ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka.
Wata tawagar kasar Jamus tare da jakadan kasar a Nijar sun kammala wata ziyarar kwana biyu a jihar Agadez dake Arewacin Nijar inda suka samu ganawa da hukumomi tare da tattaunawa game da irin ayyukan raya kasa da kuma wasu batutuwa dama
Johnson ya kasance cikin jagororin masu adawa da kafa kotun da za ta saurari kararrakin dake alaka da laifuffukan yakin da aka aikata lokacin yakin basasar Laberiya.
Hukumar Zabe ta kasar Ghana tana ci gaba da fuskantar suka daga ‘yan jarida da masu ruwa da tsaki kan shawarar takaita damar shiga cibiyoyin tattara sakamakon zabe na jihohi ga gidajen jaridu 12 kawai a zaɓen 2024, matakin da hukumar ta ce ya zama dole don tabbatar da tsari da tsaro.
Al’ummar Ghana na shirye-shiryen kada kuri’ar zaben Shugaban kasa da na ‘yan Majalisar Dokoki a ranar 7 ga Disamba.
Jami’an hukumomin shige da fice ko Douane daga kasashen Afirka ta Yamma da ta Tsakiya sun fara gudanar da taro a birnin Yamai da nufin bitar halin da ake ciki a sha’anin shige da ficen kaya a kan iyakokinsu da neman hanyoyin magance wasu matsaloli.
Daruruwan ‘yan tawaye na kungiyar MJRN dake fafutukar ganin an dawo da tsohon shugaba Mohamed Bazoum da sojoji suka kifar a shekarar 2023 da suka fito daga kasar Libiya sun ajiye makamai tare da mika wuya ga mahukuntan kasar Nijar
Wani rahoto da wata kungiya mai zaman kanta ta kasa da kasa Equality Now ta fitar, ya ce ma’anar fyade a kasashen Afirka 25 ya ba da dama ga masu aikata laifuka su tafiyarsu ba tare da an tuhumesu wani laifi ba.
Sanarwar da wata kungiya mai rajin ceton bakin haure “Migrant Rescue Watch”, ta wallafa a shafinta na X, tace an kama mutanen ne a garuruwan Sabha da Bani Walid.
A yayinda wa'adin cika shekara da ficewarsu daga kungiyar CEDEAO, ministocin cikin gidan Nijar, Mali da Burkina Faso sun amince da sabon samfarin fasfo da takardun kasa da za a fara amfani da su domin yin bulaguro a maimakon fasfon ECOWAS da ake amfani da shi a yanzu haka
Tsama tsakanin kasar Faransa da Jamhuriyar na kara zafafa, yayinda sojojin da ke mulki a kasar suka kuduri aniyar sake wallafa tarihin kasar.
Domin Kari
No media source currently available
Sojojin haya na kungiyar Wagner suna ci gaba da gudanar da ayyukansu duk da mutuwar shugabansu Yevgeny Prigozhin a watan Agustan 2023
Bayan kammala zaben shugaban kasa a Ghana, manazarta na ci gaba da yin tsokaci kan yadda aka gudanar da zaben
Wasu ‘yan uwa biyu daga Kenya suna ba da gudunmowarsu wajen kare muhalli inda suke amfani da takardun jarida wajen yin fensuran rubutu.
Zababben Shugaban Amurka Dobald Trump ya wallafa wasu sakonni a kafafen sada zumunta na barazanar kara haraji kan Canada, China da Mexico
A jihar Kano dake Najeriya ana zargin wani da cin zarafin wata ma'aikaciyar jinya mai dauke da juna biyu a asibitin yara ta Isyaka Rabiu
A Nijar an bude wata kasuwar baje koli ta ayyukan hannu da ake kira SAFEM, da matan kasar ke halarta daga jihohin da wasu kasashen Afirca