Mataimakin shugaban kasar Rigathi Gachagua ya ce yara 86 ne kawai aka gani daga cikin yara sama da 150, ya kuma bukaci al’ummar yankin da watakila suka bai wa wasunsu da ba'a gani ba mafaka da su taimaka su bayyana su.
Jami'an tsaro sun tabbatar da cewa kwaya ce da ake shirin sayar wa yan ta'adda ita.
A cewar Shugaba Xi, za a bada fiye da rabin adadin kudaden a matsayin bashi, inda za a zuba dala biliyan 11 “cikin nau’ukan tallafi daban-daban” sannan a bayar da dala biliyan 10 ta hanyar karfafa gwiwar kamfanonin China su zuba jari.
Masanan sun yi kiran ne bayan isar Karamin Ministan tsaro Bello Matawalle da Hafsoshin sojin Najeriya Sokoto don yakar 'yan ta'adda.
Kotun daukaka kara ta birnin Yamai a Jamhuriyar Nijar ta umurci mahukunta su gaggauta baiwa wasu sabbin jami’an kwastam damar fara aiki kokuma a biya su diyyar miliyan 50 na cfa a kowace rana tsawon shekaru 5.
Rukunin karshe na dakarun Jamus wanda adadinsa ya kai 120 ya kammala ficewa da kayansa daga Nijar kamar yadda Jamus ta cimma yarjejeniya da hukumomoin mulkin sojojin kasar da suka bukaci su fice kamar yadda ta kasance da sojojin Faransa da na Amurka.
Daruruwan masu fama da zazzabi suna kwance a kan siraran katifu a kasan wani wurin da aka keɓe masu jinyar cutar mpox a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, yayin da ma'aikatan asibiti ke fama da matsalar ƙarancin magunguna da kuma ƙarancin sararin daukar marasa lafiya.
Za’a iya cimma yarjejeniyar samar da alluran rigakafin har miliyan 12 ya zuwa shekara mai zuwa ta 2025, gwargwadon karfin Kamfanonin da ke harhada rigakafin, a cewar sanarwar.
Kasar Congo ce ta fi yawan kamuwa da cutar - tare da mutane 18,000 da ake zargin sun kamu, yayin da mutane 629 suka mutu.
Zaben Shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki na 2024 a Ghana na kara gabatowa, kuma manyan jam’iyyun siyasa biyu; wato NPP mai mulki da babbar jam’iyyar adawa ta NDC sun kaddamar da manufofinsu (manifestoes) game da makomar kasar ga al’ummar Ghana.
Kungiyoyin bunkasa harshen Hausa da al’adun Bahaushe a Jamhuriyar Nijar sun gudanar da bikin tunawa da ranar Hausa ta duniya kamar yadda bikin ke gudana a kasashen Hausa a wannan Litinin 26 ga watan Agusta.
Domin Kari
No media source currently available