A karshen taron da suka gudanar a birnin Bamako ministocin harakokin wajen kasashen sahel da suka hada da Nijar, Mali da Burkina Faso masu fama da matsaloli iri daya sun sanar cewa sun cimma matsaya domin yin magana da yawu guda a taron MDD na shekara shekara.
Dakarun sojin sama da na kasa sun kashe sama da maharan har su 100, bisa bayanan sojojin ba tare da wani karin bayani ba.
Babu cikakkun bayanai game da halin da yanayin tsaro ke ciki a kasar Mali a yau Laraba bayan da a jiya Talata wasu masu tada kayar baya suka afkawa kwalejin horas da jami’an ‘yan sanda da wasu muhimman wurare.
Asiedu Nketiah ya bayyana muhimmancin zanga-zangar da suke gudanarwa a duk yankuna 16 na kasar, tare da kira ga magoya baya da su jajirce wajen ganin an tabbatar da gaskiya a zaben.
Babban hafsan sojin kasar Oumar Diarra ya ce sojoji sun yi nasarar kashe maharan, amma bai bayar da cikakken bayani ba.
Goita ya fada yayin wani jawabi da aka watsa ta talabijin da yammacin ranar Lahadi cewa “A cikin kwanakin masu zuwa, za’a sanya sabon fasfo na AES da nufin daidaita takardun balaguro a yankinmu.”
A taron manema labarai da Gamayyar kafofin yada labarai kan yaki da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, kungiyoyin farar hula daban-daban sun yi kira da a dauki matakin gaggawa kan wannan al'amari.
Fafatawar mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris da tsohon shugaban kasa Donald Trump yau Talata 10 ga watan Satumba da karfe 9 na dare agogon ET da Laraba 11 ga watan Satumban da muke ciki da na safe 1 dare agogon UTC.
Hukumomin al'ummomin da ke kan iyakar Najeriya da Nijar na kokarin dakile yaduwar cutar kwalara da ta bulla a birnin N'Konni na Jamhuriyar Nijar.
Shugaban hukumar ANIE Muhammad Charfi ya shaidawa manema labarai cewa fiye da mutane milyan 5.3 ne suka zabi Tebboune, kwatankwacin kaso 94.56 cikin 100 na kuri’un da aka kada a zaben.
Domin Kari
No media source currently available