Jam’iyyar NDC ta ce Ghana na bukatar ‘saisaitawa,' domin jam’iyya mai ci ta hargitsa kasar, haka kuma jam’iyyar NPP mai mulki ta ce Ghana na bukatar ‘ingantawa’ ne kawai, domin ta yi aiki kuma za ta kara inganta aikin da ta yin, kamar yadda mataimakin shugaban kasa, kuma dan takarar shugaban kasa, Dakta Mahamudu Bawumia ya ce: ‘Ghana na bukatar ingantawa ne ba sake saisaitawa ba. Kuma na bayyana mahimman alkawarina 14 ga mutanen Ghana, domin dorewa da faɗaɗa tattalin arzikin Ghana da yake sake fasali’.
A hira da Muryar Amurka, jami’in sadarwa na jam’iyyar NPP, Alhaji Aminu Abu, ya ce idan aka yi la’akari da ayyukan da gwamnati mai mulki ta yi da kuma ababan da manufofin jam’iyyarsa su ka kunsa, lallai Ghana ba ta bukatar saiti, sai dai su kara inganta ayyukan da suka riga suka yi.
Sai dai tsohon shugaban kasa, kuma dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta NDC, Dakta John Mahama, ya kara jaddada cewa, manufofin da jam’iyarsa ta NDC ta kaddamar za ta saisaita kasar ne domin ba a inganta abin da ya lalace, ‘Wani ya ce ingantawa, amma ta yaya za a inganta abin da ya riga ya lalace? Kuma idan mu ka yi magana game da sake saiti ba kawai batun tattalin arziki ba ne, shi ya sa a taron kaddamar da manufarmu ba a kan tattalin arziki kadai na yi Magana ba’.
Alhaji Mohammed Nazir Saeed, jami’in sadarwa na jam’iyyar NDC ya ce lallai Ghana na bukatar a sake yi mata saiti, domin haka ne suka tsara manufofinsu yadda zai dace da hakan.
Wasu al’ummar sun bayyana mabanbantan ra’ayi kan tasirin da manufofin ‘yan takaran za su yi ga kuri’ar da za su kada a zabe mai zuwa. Haka kuma wasu suka bayyana rashin yardarsu ga alkawuran da jam’iyu ke yi a cikin kundin manuofinsu.
Sai dai masana kamar babban darektan gidauniyar kafafen yada labarai na Africa ta yamma (MFWA), Sulaiman Braimah, na da ra’ayin cewa, makomar Ghana ba ta dogara da hasashen manufofin ‘yan takara. Abin da ake bukata shi ne jagoranci na gaskiya, da rikon amana; wanda al’ummar yanzu da masu zuwa za su rika tunawa da su a kan yadda suka yi wa kasa hidima.
Saurari cikakken rahoton Idris Abdullahi:
Dandalin Mu Tattauna