Matasa sama da 100 ne aka ayyana cewa sun yin nasara daga cikin wadanda suka rubuta jarabawar shiga aikin kwastam da gwamnatin Nijar ta shirya a shekarar 2018 sai dai bayan kammala daukan horo baiwa wadanan sabbin jami’ai dama su fara aiki ya ci tura.
Kawo yanzu hukumomi ba su bayyana matsayinsu ba dangane da wannan al’amari da suka gada daga shudeddiyar gwamnatin farar hula wanda kuma ko a wancan lokaci ba a taba fitowa fili aka bayyana ainihin dalilin turjiyar da ke tattare da batun shigar da wadanan sabbin jami’ai a sahun ma’aikata ba.
Sakataren hadaddiyar kungiyar kwadago ta CNT Mounkaila Halidou na cewa ya zama wajibi gwamnati ta bi umurnin kotu don kada a ja wa kasa asarar kudade.
Wani rukunin na daban na irin wadanan ma’aikata da ke kunshe da sabbin sufetocin ma’aikatar kwastam sama da 50 da suka ci jarabawa a shekarar 2020 na ci gaba da jira a ba su damar soma aiki bayan kammala daukan horo.
Su ma turjiyar da wancan rukuni ke fuskanta ita ce ta rutsa da su koda yake wasu na ganin yiwuwar za ta canza zane a bisa la’akari da manufofin gwamnatin mulkin soja ta CNSP.
A saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna