Hukumomim Burkina Faso sun ce sun yi nasarar dakile wasu hare-haren ta’addancin da aka yi yunkurin kai wa a lokaci guda a wasu mahimman wuraren birnin Ouagadougou ciki har da fadar shugaban kasa.
Ambaliyar da ake fama da ita sakamakon ruwan da ake tafkawa a jamhuriyar Nijar ya yi sanadin daga ranar komawar dalibai ajin karatu zuwa 28 ga watan Oktoban dake tafe a maimakon 1 ga wata.
A yau Litinin, hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa, ta samu rahotannin cewar kimanin mutane dubu 30 ne suka harbu da cutar kyandar biri a nahiyar Afirka a bana, galibinsu a jamhuriyar dimokradiyyar Congo inda gwaje-gwaje suka kare.
Gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar ta bayyana shirin karfafa matakan tsaro a yankunan da ke karkashin dokar ta baci, bayan la’akkari da yadda ‘yan ta’adda suka zafafa kai hare-hare a ‘yan kwanakin nan.
Kwararrun sun ce, hare-haren na ranar Talata a Bamako, su ne irinsu na farko cikin shekaru da dama, kuma sun yi mummunar illa ga gwamnatin mulkin soja da ke mulki a kasar.
A karshen taron da suka gudanar a birnin Bamako ministocin harakokin wajen kasashen sahel da suka hada da Nijar, Mali da Burkina Faso masu fama da matsaloli iri daya sun sanar cewa sun cimma matsaya domin yin magana da yawu guda a taron MDD na shekara shekara.
Dakarun sojin sama da na kasa sun kashe sama da maharan har su 100, bisa bayanan sojojin ba tare da wani karin bayani ba.
Babu cikakkun bayanai game da halin da yanayin tsaro ke ciki a kasar Mali a yau Laraba bayan da a jiya Talata wasu masu tada kayar baya suka afkawa kwalejin horas da jami’an ‘yan sanda da wasu muhimman wurare.
Asiedu Nketiah ya bayyana muhimmancin zanga-zangar da suke gudanarwa a duk yankuna 16 na kasar, tare da kira ga magoya baya da su jajirce wajen ganin an tabbatar da gaskiya a zaben.
Babban hafsan sojin kasar Oumar Diarra ya ce sojoji sun yi nasarar kashe maharan, amma bai bayar da cikakken bayani ba.
Goita ya fada yayin wani jawabi da aka watsa ta talabijin da yammacin ranar Lahadi cewa “A cikin kwanakin masu zuwa, za’a sanya sabon fasfo na AES da nufin daidaita takardun balaguro a yankinmu.”
Domin Kari
No media source currently available