Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

UNICEF, WHO DA CDC Suna Hadin Gwiwar Samar Da Rigakafin Kyandar Biri


Za’a iya cimma yarjejeniyar samar da alluran rigakafin har miliyan 12 ya zuwa shekara mai zuwa ta 2025, gwargwadon karfin Kamfanonin da ke harhada rigakafin, a cewar sanarwar.

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya fitar da bukatar gaggawa ta samar da rigakafin cutar kyandar biri ga kasashen da ke fama da rikici tare da hadin gwiwar kawancen rigakafin Gavi, da hukumar kula da cutuka ta Afirka CDC, da kuma Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, kamar yadda kungiyoyin suka bayyana a cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa a ranar Assabar.

Za’a iya tsara yarjejeniyar samar da alluran rigakafin har miliyan 12 ya zuwa shekara mai zuwa ta 2025, gwargwadon karfin Kamfanonin da ke harhada rigakafin, a cewar sanarwar.

Sanarwar ta ce Karkashin kwangilar, UNICEF za ta shata ka’idodin yarjejeniyar ta samar da rigakafin tare da kamfanonin yin alluran rigakafin.

Wannan zai baiwa UNICEF damar siya da jigilar alluran rigakafi ba tare da bata lokaci ba, da zarar an tabbatar da kudade, buƙatu, tsare-tsare da kuma ka’idodi.

Sanarwar ta kara da cewa WHO na nazarin bayanan da masana'antun suka gabatar a ranar 23 ga watan Agusta, kuma tana sa ran kammala bitar bayanan domin gaggauta soma amfani da ita nan da tsakiyar watan Satumba.

A farkon watan Agusta, hukumar ta WHO ta ayyana annobar kyandar biri a matsayin matakin gaggawa na kiwon lafiyar jama'a a duniya bayan barkewar cutar a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, wadda ta bazu zuwa kasashe makwabta.

An sami fiye da mutane 18,000 da ake zargin sun kamu da cutar a Kongo a wannan shekara, tare da mutuwar mutane 629, yayin da aka tabbatar da sama da mutane 150 a Burundi, in ji Darakta Janar na WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG