Kungiyoyin farar hula da suka hada da Gamayyar kungiyoyin Kwadago da na addinai da Gamayyar kafofin yada labarai na Ghana, suna kara nuna matsin lamba ga gwamnati da ta gaggauta yaki da hakar ma'adinai (Galamsey) ba bisa ka'ida ba domin mummunan tasirin da hakan ke yi ga koguna, samar da ruwan sha, muhalli, lafiya, da kuma noma.
Kungiyoyin sun kara kaimi ne bayan da masana suka ba da gargadin cewa, in ba a yaki hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, da aka fi sani da Galamsey a nan Ghana, cikin gaggawa ba, to Ghana za ta kai ga shigo da ruwan sha daga kasashen waje.
Biyo bayan wannan kuma kamfanin ba da ruwa na Ghana ya fitar da sanarwar cewa gurbacewar tafkuna da koguna, a sanadiyar ‘Galamsey’ ya sa ba a iya samar da ruwa mai inganci ga mazauna birnin Cape Coast da kewaye dake yankin tsakiya.
Baya ga gurbata ruwan sha da ‘Galamsey’ ke yi, Mohammed Jafar Dankwabia, mataimakin darektan bincike ne a Cibiyar kula da yanayi da kiyaye abinci, ya yi wa Muryar Amurka karin bayani game da wasu illar da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba ke yi wa Ghana.
Ya ce, Sinadaran suke amfani da su, suna lalata gonaki da ruwan da ake amfani da shi wurin ban ruwa. Domin haka, “Aikin ‘Galamsey’ na da matsala sosai, kuma idan ba mu tsaya ba, nan gaba idan bamu shigo da abinci (daga waje ba) ba za mu iya shuka namu ba; ba za mu samu ingantaccen ruwa mu sha ba; kuma rayuwa za ta yi mana wuya”.
A taron manema labarai da Gamayyar kafofin yada labarai kan yaki da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, kungiyoyin farar hula daban-daban sun yi kira da a dauki matakin gaggawa kan ‘Galamsey’.
Kenneth Koomson, Mataimakin sakataren gamayyar kungiyoyin ‘yan kwadago, ya bayyana cewa, Kungiyar ta bukaci a gaggauta kafa dokar ta-baci a yankunan da lamarin ‘Galamsey’ ya shafa, tare da dakatar da duk wani aikin hakar ma'adinai a gandun dazuzzuka, da kafa kotuna na musamman domin hukunta masu laifi, sannan a tura sojoji domin tarwatsa kayan aikin hakar ma'adinai.
Ya kara da cewa: “Ma'aikata za su fara gudanar da zanga-zanga, da kuma yajin aikin a duk fadin kasar, idan gwamnati ta kasa magance matsalolin da muka shimfida, a karshen Satumba 2024”.
Shi kuma Jagoran Gamayyar Kungiyoyin Kafafan Yada Labarai kan
Yaki da ‘Galamsey’, Dokta Ken Ashigbey, yace a matsayinsu na kafafen yada labarai, ba za su yada duk wani labari da zai zo daga ma’aikatar Filaye da Albarkatun Kasa ba, “Idan aka fara yajin aikin, za mu yi watsi da duk wani abu da ma’aikatar filaye da albarkatun kasa za su yi. Don haka muna addu'ar shugaban kasa ya yi abinda ya dace.
Shugaban kungiyar ‘yan jarida ta Ghana (GJA), Mista Albert Kwabena Dwumfour a nasa bangaren ya gargadi yan takaran shugaban kasa a zabe mai zuwa da su tabbatar sun goyi bayan wannan tafiyar ta yaki da Galamsey, “Idan har suka kasa yin hakan, hakan na nuni da cewa ba su da muradin al’ummar kasar kuma ba su cancanci shugabanci ba.”
Kungiyar kananan manoma ta Ghana (PFA), ta yi kira ne da a kara har da kananan masu hakar ma’adinai da gwamnati ta ba su lasisi a cikin wadanda za a hana aikin hakar ma’adinan.
Amma, Sai dai mai tsara shirye-shirye na kungiyar kananan masu hakar ma’adinan, ya yi watsi da wannan kiran domin suna da lasisi, kuma gwamnati ta kafa su ne domin matasa su samu aikin yi. Yace, suna da maikata a karkashinsu kimanin miliyan 1.8. Idan an dakatar da su, duka za su rasa aikinsu ke nan.
Sauran kungoyi da suka kara muryoyinsu kan yaki da galamsey sun hada da kungiyar masu gudanarwa mata (EWN), da kungiyar kananan mahakar ma’adinai na Ghana, da kungiyar kafofin yada labarai masu zaman kan su, da kungiyar buga jaridu da masu yada labarai ta yanar gizo da sauransu.
Dandalin Mu Tattauna