Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kalli Muhawarar 'Yan Takarar Shugaban Amurka Kai Tsaye A Kan Voahausa.Com


Fafatawar mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris da tsohon shugaban kasa Donald Trump yau Talata 10 ga watan Satumba da karfe 9 na dare agogon ET da Laraba 11 ga watan Satumban da muke ciki da na safe 1 dare agogon UTC.

An shirya tsaf ana jiran zuwan al'amarin da ake yiwa kallon mafi mahimmanci a yakin neman zaben da zai share fagen zaben shugaban Amurka da zai gudana a ranar 5 ga watan Nuwamba mai zuwa.

Muhawarar da za'a fafata tsakanin mataimakiyar shugaban amurka 'yar jam'iyyar Democrat Kamala da abokin hamayyarta tsohon shugaban kasa Donald Trump a daren yau talata.

'Yan takarar 2 basu taba haduwa da juna ko yin magana ta wayar tarho ba, amma a yau Talata zasu tsaya daf da juna a Cibiyar Tsarin Mulkin Kasa dake birnin Philadelphia.

Sun shirya tsaf domin yin musayar yawu da juna tsawon mintuna 90 yayin da zasu rika amsa tambayoyin da masu karanta labarai a tashar talabijin ta ABC; David Muir da Linsey Davis za su rika jefa musu.

Dimbin milyoyin Amurkawa ne ake sa ran su kalli mahawarar da 'yan takarar shugabancin Amurka 2 zasu tafka a al'amarin daka iya zama mahawara daya tilo a yakin neman zaben.

Mahawarar na zuwa ne makonni 8 gabanin ranar zaben da gwamnati ta tsayar sai dai kwanaki kadan gabanin wa'adin da aka amincewa masu zabe da wuri su fara kada kuri'a a wasu daga cikin jihohin kasar 50.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG