Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sami Bullar Cutar Kwalara Kan Iyakar Najeriya Da Nijer


Cutar Kwalara A Kamaru
Cutar Kwalara A Kamaru

Hukumomin al'ummomin da ke kan iyakar Najeriya da Nijar na kokarin dakile yaduwar cutar kwalara da ta bulla a birnin N'Konni na Jamhuriyar Nijar.

A daidai lokacin da a ke cigaba da shata ruwan sama kamar da bakin kwarya a Jamhuriyar Nijer, da ya haifar da ambaliya da dama a sassan kasar, yayin da jama'a da dama suka rasa matsugunnan su. Tuni dai hukumomin da ke da alhakin fitar da kididiga game da hasarorin da ambaliyar ruwan ta haifar a kasar ta sanar da cewa, yanzu haka, sama da mutane 10.000 ne suka rasa muhallan su, yayin da sama da mutane 200 suka rasu.

A halin da ake ciki kuma, an samu bullar kwalara a kan iyakar Nijer da Najeria a cikin garin Birni N'Konni, kamar yanda shugabar hukumar assibitin Birni N'Konni Docteur Nana Mariama Maman ta bayyana wa Muryar Amurka.

BORNO: Masu bada allurar rigkafin cutar kwalara
BORNO: Masu bada allurar rigkafin cutar kwalara

Hukumomin garin da jami'an kiwon lafiyar gundumar sun bayyana gano wata unguwa dake cikin garin da cewa, can ne suke tunanin abin ya samo asuli a cikin garin na Birni N'Konni.

Tuni dai, 'yan Najeriya dake kan wannan iyakar suka soma kira ga hukumomin garuruwan dake wannan gefen na Najeriya, da su dauki dkkan matakan da suka dace domin kare yankin daga bullar cutar.

Wannan matsalar ta bullar allobar kolera a Birni N'Konni ta shafi mutane 7 yayinda magajin garin yace jami'an kiwon lafiya na kokarin dakile wannan lamarin da ya sa, hukumomin asibiti na kasa da na jahar Tahoua isa a garin na Birni N'Konni bisa umurnin Shugaban kasar Nijer Jeneral Birgediya Abdurahamane.

Saurari cikakken rahoton Harouna Mammane Bako:

An Sami Bullar Cutar Kwalara Kan Iyakar Najeriya Da Nijer
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:46 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG