Wannan dai na faruwa ne kwanaki biyu bayan da shugaba Puttin da Barrack Obama suka cimma matsaya a birnin New York
Kenyatta ya ce yin hakan zai kai ga samar da cibiyar ayyukan jinkai a Sudan Ta Kudu, inda tashin hankalin ya tilasta mutane wajen miliyan 2 barin gidajensu
Yan kasar Cameroon 21 ne aka tabbatar sun rasu kana 123 ne suka samu raunuka daban-daban kana 77 ne suka bace kawo yanzu babu labarin su
Manufar taron dai shine tunatar da manema labarai illar anfani da munanan kalamai da ka iya haifar da tunzuri tsakanin al’umma mabanbanta, da addinai da zafafan kalamai da kuma yin yarfen siyasa.
Taron majilisar dinkin duniya na wannan shekarar ya fara ne da gagarumin taron koli akan bunkasa da kara tabbatar da shirin muradun karni, na yaki da talauci, yunwa, ciwo, koma bayan mata, da kananan yara, da ilmi da sauran su
Har yanzu ana ci gaba da tantance adadin mutanen da suka mutu na kasashe daban-daban wadanda turmutsin nan ya rutsa dasu a kasar Saudiyya.
Wani masani a fannin tattalin arziki yace Bankunan kasuwanci zasu nemi hanyoyin rayuwa idan aka fara aiwatar da umarnin shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari na ajia a banki daya.
Dan takaran shugaban kasa na Amurka a karkashin lemar jam’iyyar Republicans, attajirin nan Donald Trump ya sha sukar lamiri kusan daga kowane bangare a lokacin muhawara ta biyu da aka gudanar a tsakanin abokan takaran nashi,
Rundunar sojan kasar Burkina Faso tace ta kwace ragamar mulkin kasar kuma har ta nada wani babban hafsan sojan don ya jagoranci sabuwar majalisar mulkin da suka kafa don tafiyarda kasar.
Sakamakon wani sabon bincike da aka gudanar, ya nuna cewa, mutanen da ke zaune a kusa da madatsun ruwa na fuskantar barazanar saurin kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro sau hudu fiye da wadannan ba sa zaune a kusa da dam din a kasashen da ke Kudu da Hamada a Afrika.
Domin Kari