Taron majilisar dinkin duniya na wannan shekarar ya fara ne da gagarumin taron koli akan bunkasa da kara tabbatar da shirin muradun karni, na yaki da talauci, yunwa, ciwo, koma bayan mata, da kananan yara, da ilmi da sauran su
Har yanzu ana ci gaba da tantance adadin mutanen da suka mutu na kasashe daban-daban wadanda turmutsin nan ya rutsa dasu a kasar Saudiyya.
Wani masani a fannin tattalin arziki yace Bankunan kasuwanci zasu nemi hanyoyin rayuwa idan aka fara aiwatar da umarnin shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari na ajia a banki daya.
Dan takaran shugaban kasa na Amurka a karkashin lemar jam’iyyar Republicans, attajirin nan Donald Trump ya sha sukar lamiri kusan daga kowane bangare a lokacin muhawara ta biyu da aka gudanar a tsakanin abokan takaran nashi,
Rundunar sojan kasar Burkina Faso tace ta kwace ragamar mulkin kasar kuma har ta nada wani babban hafsan sojan don ya jagoranci sabuwar majalisar mulkin da suka kafa don tafiyarda kasar.
Sakamakon wani sabon bincike da aka gudanar, ya nuna cewa, mutanen da ke zaune a kusa da madatsun ruwa na fuskantar barazanar saurin kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro sau hudu fiye da wadannan ba sa zaune a kusa da dam din a kasashen da ke Kudu da Hamada a Afrika.
Biyo bayan wani tashin bam da ya afku a sansanin 'yan gudun hijira da ke Malkohi wanda ya yi sanadiyyar rasa rayuka da dama, lamarin ya kara tada hankalin 'yan gudun hijirar.
Kasashen Rasha da Angola sun takawa kudurin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya akan Sudan ta Kudu birki
Jeremy Corbyn wanda da farko ba a zaci zai c kai labari ba, lokacin da ya tsaya takarar shugabancin jam’iyar Labor a Birtaniya ya lashe zabe
mataimakiyar sakataren ma'aikatar harkokin wajen Amurka tace ba za a dage takunkumin da aka sawa Rasha ba sai an aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma kan rikicin Ukrraine baki daya.
Domin Kari