Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fadada Yarjejeniyar Zaman Lafiya a Sudan Ta Kudu- In Ji Uhuru Kenyatta


Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya ce ya kamata kasashen gabashin Afirka da su ka taimaka aka sake cimma yarjajjeniyar zaman lafiya a Sudan Ta Kudu, su fadada wannan hobbasar ta hada da sa bakin al'ummar duniya wajen aiwatarwa, saboda a samu kawo karshen yakin da aka shafe watanni 20 ana yi.

A wata hirarsa da VOA Africa 54 a birnin New York, Kenyatta ya ce yin hakan zai kai ga samar da cibiyar ayyukan jinkai a Sudan Ta Kudu, inda tashin hankalin ya tilasta mutane wajen miliyan 2 barin gidajensu. Zai kuma taimaka wajen kafa gwamnatin hadin kan kasa tsakanin gwamnati mai ci da kuma 'yan tawaye.

Kenyatta ya jaddada bukatar kar a kyale gwamnati da 'yan tawaye kawai a al'amarin, amma a hada da kungiyoyin sa kai, da Majami'u da sauran al'ummomin Sudan Ta Kudu din.

Yarjajjeniyar da aka cimma a watan jiya, ta tanaji daina harkokin soji a Juba, babban birnin kasar, da kafa gwamnatin hadin kan kasa ta wuccin gadi cikin kwanaki 90 da kuma bai wa 'yan tawaye matsayin Mataimakin Shugaban Kasa. To amma tun bayan da aka rattaba hannu kan yarjajjeniyar, dukkan bangarorin biyu sun saba ma 'yarjajjeniyar.

XS
SM
MD
LG