Taro na goma sha shida na kwamitin shugabanin ‘yan sanda dake gudana a birnin Yaounde ya hada kasashen Afirka ta tsakiya baki daya da Congo, Gabon, Chadi jamhuriyar Afirka ta tsakiya Kamaru da Sao Tome and Principe.
Masu sada zartarwa dokoki na kasashen Chadi Gabon da Faransasuke wannan tattaunawar.
Wannan taron yana basu damar tattaunawa ne kan harkan tsaron kan iyakoki na kasashen tare da duba irin abubuwan da aka yi a baya.
Cikin irin abubuwan da aka fahimta akwai shigo da magunguna wanda bana kwarai bane da shigo da makamai dake bada ga kafuwar kungiyoyin tawaye da ‘yan ta’adda in ji wani mai halartar wannan taron.
Bayan wadannan matsalolin kasashen na fuskantar yaki da ‘yan ta’adda da masu fashi da makami da kuma barayin shanu da masu fataucin sassan dan Adam.