Shugaban kasar Cameroon Paul Biya ya mika taaziyyar sa ga iyalan wadanda suka rasu kana ya aikawa sarkin Saudiyya nasa gaisuwan taaziyya, kuma yace ofishin kasar ta Cameroon dake kasar ta Saudiyya zasu yi kokarin samun labarin wadanda ba a gani ba har yanzu.
Wakilin sashen Hausa a Cameroon Muhammadu Awal Garba ya tambayi Usman Yusuf jagoran aikin Hajji na kasar kome zai ce game da wannan hadarin?
‘’Rashin natsuwa da rashin bin tsari shine zai kawo ga haka wadansu daga cikin yan uwa ne domin kasan tsari da akayi a wannan wuri wurin jifar shaidan hanyar da masu shiga suke masu fita ba zasu hada dasu ba, to sai aka zo aka samu yadda hanyoyin suke haduwa sai suka samu wata hanya ta dan buda sai suka nemi su bi wadannan suna dawo wa, su kuma suka shiga to da masu tsaro kuma suka ga hakasai suka rufe domi kar sauran jamaa su shiga a rufewan da suka yin nan ne fa masu zuwa ta bayan sai suna hawa kan wadancan to anan ya kawo wa mutane wannan hatsarin har wasu babu nunfashi da sauran su aka soma hawa kan wadansu su kuma jamiaan tsaro da masu kula da wurin abin yazo yafi karfin su.’’
Ga Muhammad Awal Garba da ci gaban labarin ‘’3 47’’