Kimanin kasashe 200 ne dake da wakilci a Majilisar dinkin duniya suka rattaba hannu akan sabon kudiri na wannan yaki nan da shekara ta 2030 anan shalkwatar majilisar dinkin duniya dake birninNew York.
Shugaban kasar Uganda Youweri Musseveni shine daya daga cikin shugabannin dake shugabantar taron kolin kuma ya tabbatar wa shugabannin duniya irin matakin da shugabannin suka dauka.
‘’Yace a bakin dayan mu muna aika sakon mu zuwa ga mutanen karkara birane da dukkan kasashen duniya cewa, mun himmatu wajen daukar muhimmam matakai da kyautata rayuwar su’.
Alasan Yusha Babul Wais mai sharhi ne akan harkokin yau da kullun kuma ya halarci wannan taron kuma ya bayyana raayin sa game da daya daga cikin matakan cimma wannan muradun.
‘’Matakin da a dauka shine yaya za ayi su wadannan tsarin ya sauya rayuwar mutane, yaya za yi dukkan mutanen duniya su samu labara, idan dai mutane suka samu labari ga abinda ake dauka ga abinda ake dauka ga abinda ake saurare to zasu sa hankali suyi ta dakon gwamnati su aini tabbatar cewa ana cimma buri ko kuma ba cimmawa, wannan ko zai bayyana tasamun labarai’’
Ga Baba Yakubu da ci gaban labarin ‘’3 09’’