An zabi Jeremy Corbyn wani mai matsanancin ra’ayin sauyi, a matsayin shugaban jam’iyar Labor jiya asabar, nasarar da ake gani zata shafi matsayin Birtaniya a Kungiyar Tarayyar Turai, matakin da wani tsohon firai ministan jam’iyar Labor yace zai iya sa jam’iyar ta rasa goyon baya.
Magoya bayan Corbyn sun yi ta murna a shelkwatar jam’iyar, yayinda ‘yan gani kasheni a duk fadin kasashen Taurai kuma suka yaba zaben nasa.
Akwai sabanin ra’ayi dangane da zaben nashi inda wadansu suke fargaban cewa, masu zabe zasu guji jam’iyar sabili da tsare tsarensa masu tsauri da suka hada da yin gaban kai a batun raba kasa da makaman nukiliya, batun zama dan kasa da kuma gabatar da tsarin yiwa attajirai haraji.
Corbyn wanda da farko ba a zaci zai ci zabe ba, a lokacin da ya tsaya neman shugabancin jam’iyar, ya fada a jawabinsa bayan zabe cewa, abubuwa suna iya sauyawa, zasu kuma sauya.
Ya sami kashi 58 da digo biyar cikin dari na kuri’un, fiye da abinda aka taba zata.
Nasarar da ya samu ta nuna irin goyon bayan ‘yan gurguzu a kasashen turai, tare da lashe zaben Syriza a Girka cikin watan Janairu da kuma irin goyon bayan da jam’iyar dake adawa da tsuke bakin aljihu take samu a kasar Spain. Dukan jam’iyun sun yi na’am da zaben