Jiya Talata kasashen Rasha da Angola sun dakatar da yunkurin da kwamitin sulhu Majalisar Dinkin Duniya yaso dauka na azawa wadansu shugabannin gwamnati da na 'yan tantawaye takunkumi a Sudan ta Kudu.
Wannan mataki yana zuwa ne a dai dai lokacin da kungiyoyin da suke rajin kare 'yancin Bil'Adama uku, Enough Porject da Human Rights Watch, da Amnesty International suke kira ga kwamitin sulhun ya kakabawa wasu mutane takunkumi wadanda ake zargi da aikata wasu laifuffuka da cin zarafin Bil'Adama a Sudan ta Kudu.
Wata jami'ar kungiyar kare hakkin Bil"Adama da ake kira Enough Porject, Lindsey Hutchison, tace bata ji dadin matakin da Rasha da Angola suka dauka ba. Tace hana daukan wannan mataki zagon kasa ne ga alkawarin da kwamitin sulhun yayi na azawa duk wani mutum da yake neman hana ruwa gudu na ganin an sami zaman lafiya a kasar.