A cikin jawabinsa wajen kaddamarwar da aka gudanar a garin Kaduna, Mai Martaba Sarkin Musulmi ya yi kira ga gwamnatoci su rika taimakawa mabukata, yayinda kuma ya gargadi mahajjata subi umarnin hukumomi a kowanne mataki.
Sarkin Kano, Mal Sanusi na biyu wanda zai jagoranci kwamitin gwamnatin tarayya a aikin hajin bana, ya hori mahajjata suji tsoron Allah wajen gudanar da aikin hajji tare kuma da addui’ar zaman lafiya a Najeriya.
A cikin jawabinsa, mai masaukin baki, gwamnan jihar Kaduna Nasiru el-Rufa’I wanda kuma ya wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari, shima ya jadada bukatar kiyaye doka da oda yayin gudanar da ayyukan hajji.
Ana kyautata zaton mutane dubu saba’in da shida ne zasu gudanar da aikin hajjin bana daga Najeriya, da kuma jami’ai dari takwas da hamsin, yayinda kamfanoni shida zasu yi amfani da jirage goma sha uku wajen jigilar alhazai.
Ga rahoton da wakilin Sashen Hausa Nasiru Yakubu Birnin Yaro ya aiko daga Kaduna, Najeriya.