Ta kuma yi amfani da wannan dama wajen shawartar hukumomin CNSP su amince da shawarwarin da ECOWAS ta tsayar a karshen taronta na Lahadi 10 ga watan Disamba.
Yayin da wasu kungiyoyin goyon bayan Majalisar CNSP ke kiraye kirayen ganin Nijar ta fice daga ECOWAS a matsayin martani kan takunkumomin da kungiyar ta kakaba wa kasar, masana sun gargadi hukumomin mulkin sojan Nijar su yi watsi da irin wannan shawara don kauce wa jefa kasar cikin yanayin kadaici.
Shugaban gwamnatin mulkin sojan jamhuriyar Nijar Janar Abdourahamane Tchiani ya bayyana matsayinsa dangane da sharudan da kungiyar CEDEAO ta gindaya a karshen taron da shugabaninta suka gudanar ranar lahadi, a cewarsa da dadewa Nijar ta cike ka’idodin da aka shimfida mata game da wannan dambarwa.
A jamhuriyar Nijar ‘yan kasar sun bayyana ra’ayoyi mabambanta dangane da matsayar da shugabannin kasashen kungiyar CEDEAO su ka cimma a karshen taron da suka gudanar a ranar Lahadi, dangane da rikicin siyasar da ya biyo bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata.
A yayinda shugabanin kasashen yammacin Afrika membobin kungiyar ECOWAS ke shirin gudanar da taro a gobe Lahadi 10 ga watan Disamba a Abuja domin yin nazari kan mataki na gaba kan sojojin juyin mulkin Jamhuriyar Nijar, kungiyoyin fararen hula kasar sun bukaci ECOWAS ta tausaya wa talakka.
Al'ummar Jamhuriyar Nijar sun fara maida martani bayan da kotun ECOWAS a zamanta a yau Alhamis ta kori karar da hukumomin mulkin sojan kasar suka shigar da nufin kalubalantar jerin takunkumin da kungiyar ta kakaba wa Nijar sanadiyar juyin mulkin 26 ga watan Yuli.
Jamhuriyar Nijar da kasar Mali sun bada sanarwar yanke huldar sassaucin harajin da suka kulla da Faransa a karkashin wasu yarjeniyoyin da aka rattaba wa hannu yau shekaru sama da 50 din da suka gabata.
Sabuwar jakadiyar Amurka ta gabatar wa hukumomin rikon kwaryar Nijar takardun kama aiki, kwana daya bayan haka Rasha ta tura karamin ministanta na tsaro zuwa birnin Yamai, ziyarar da masana suka fassara a matsayin wani yunkuri na Rasha na samun matsuguni a Yankin Sahel.
Shugaban Majalissar Sojojin juyin mulkin Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani na ziyarar aiki ta wuni 1 a kasashen Mali da Burkina Faso a wannan Alhamis 23 ga watan Nuwamba.
Hukumomin Mulkin sojan Jamhuriyar Nijar sun bayyana rashin jin dadi game da hukuncin kotun kasashen yammacin Afrika rainon Faransa UEMOA ta yanke dangane da bukatar janye takunkumin da kungiyar ta kakaba wa Nijar din da na ECOWAS a washe garin juyin Mulkin 26 ga watan Yuli.
Dakarun tsaron jamhuriyar Nijar sun yi nasarar hallaka ‘yan ta’adda sakamakon wata arangamar da suka yi a gundumar Sanam ta jihar Tilabery. Lamarin ya faru ne ranar Alhamis 16 ga watan Nuwamba jim kadan bayan da ‘yan bindigar suka kona wata makarantar boko a kauyen Maichilmi.
Kotun daukaka kara ta birnin Yamai a Jamhuriyar Nijar ta fara zaman shari’ar da ke tsakanin gwamnatin kasar da Janar Salou Souleyman wanda aka garkame a gidan yari a watan Disamban 2015 tare da wasu hafsoshin soja da fararen hula a bisa zargin yunkurin juyin mulki, zargin da suka sha musantawa.
Hukumomin mulkin sojan jamhuriyar Nijer sun taya takwarorin aikinsu na Mali murnar samun nasarar sake kwato garin Kidal daga hannun ‘yan tawayen arewacin kasar.
Kungiyar matasan lauyoyi ( AJAN) a Jamhuriyar Nijar ta nuna damuwa game da yawaitar kame -kamen mutane tare da tsare su ba a kan ka’ida ba duk da cewa sojojin da suka yi juyin mulki a watan Yulin 2023 sun sha alwashin mutunta yarjeniyoyin kasa da kasar da Nijar ta saka hannu.
Rundunar mayakan Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa an fara cin karfin ayyukan kwashe dakarun Faransa daga kasar ta Nijar.
Domin Kari