Cece-kuce ya barke bayan da wasu 'yan jam’iyyar PNDS na kusa da tsohon shugaba Issouhou Mahamadu suka fara zagaya jihohin Nijar don tsara gangamin goyon bayan gwamnatin sojan kasar, lamarin da magoya bayan Bazoum ke kallo a matsayin wanda ke gaskanta zargin hannun Issouhou a juyin mulkin watan Yuli.
Shugaban Faransa Hukumomin mulkin sojan Nijar da jami’an fafutuka sun maida martani bayan da shugaban Faransa ya bayyana shirin dauke jakadan kasar daga birnin Yamai zuwa gida.
Wannan shi ne karo na biyu da tsohon shugaban na Nijar yake bayyana matsayinsa a game da abubuwan da ke wakana a kasar bayan da sojoji suka ba da sanarwar juyin mulki.
Hukumomin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar sun tisa keyar wasu mukarraban hambararriyar Gwamnatin kasar zuwa gidajen yari daban-daban a jihohin Tilabery da Yamai, yayin da aka ba da sanarwar kafa wata sabuwar hukumar yaki da cin hanci da farautar mahandama dukiyar kasa.
Hambararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum ya shigar da sojojin da suka yi juyin mulki kara a kotun ECOWAS/CEDEAO sakamakon zargin tsare shi da iyalinsa ba akan ka’ida ba.
Wasu ‘yan siyasa daga jam’iyyar Democrat a Amurka sun bukaci sakataren harkokin wajen Amurka da jakadiyar Amurka a Majalisa Dinkin Duniya su yi amfani da damar babban taron Majalisar Dinkin Duniya don tuntubar shugabanin kasashen CEDEAO kan bukatar sassauta takunkumin da kungiyar ta kakaba wa Nijar.
Ma’aikatar cikin gidan Nijar ta umurci gwamnoni su zuba ido kan ayyukan tantance mutanen da zasu wakilci al’umomin kananan hukumomi a babban taron kasa da ke tafe, da nufin tattaunawa kan sabuwar turbar da ya kamata a dora kasar bayan shekaru sama da 30 da kafa dimokradiyya a kasar.
Wato kotu a jamhuriyar Nijar ta ba da belin madugun ‘yan adawa Hama Amadou bayan da ya gabatar da kansa a gaban hukumomi sa’oi kadan da komawarsa gida bayan shafe shekaru biyu ya na gudun hijira a kasashen waje.
Tsohon Firai Ministan Nijar Hama Amadou da ke hijira a kasashen waje ya koma gida da nufin bada gudunmowa a kokarin fitar da kasar daga dambarwar siyasar da ta biyo bayan juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023.
Gwamnatin mulkin sojan jamhuriyar Nijar ta ba da sanarwar yanke yarjejeniyar ayyukan soja da jamhuriyar Benin sakamakon zargin makwabciyar kasar da saba alkawari.
Gwamnatin rikon kwaryar Jamhuriyar Nijar ta tsige Shugaban hukumar ‘yan sandan birnin Yamai kwanaki kadan bayan da ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda wasu daga cikin masu zanga-zangar nuna bukatar ficewar sojan Faransa ke wuce gona da iri har ma da yin fatali da doka.
Sojojin juyin mulkin Jamhuriyar Nijar sun zargi kasar Faransa da soma shirye-shiryen kai farmaki a kasar da hadin gwiwar kungiyar ECOWAS/CEDEAO kamar yadda suka kudiri aniyyar yi a baya da nufin mayar da hambararen shugaban kasa Mohamed Bazoum kan kujerarsa.
Kungiyoyin kare hakkin jama’a a fannin makamashi mambobin gamayyar CODDAE A Jmhuriyar Nijer sun kudiri aniyar shigar da kara a gaban kotu saboda zargin Najeriya da yin fatali da yarjejeniyar kasuwancin da ke tsakaninta da Nijer a fannin makamashi.
Hukumar ‘yan sandan birnin Yamai ta umurci jagarorin masu zanga-zangar adawa da zaman sojan Faransa a kasar su mutunta doka, bayan rahotanni sun ce wasu na fakewa da sunan zaman dirshan din don tafka ta’asa, ciki har da yi wa mata fyade.
Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun ba da sanarwar kama tufafin sojan Burkina Faso a cikin motar wani sojan Faransa lokacin da ya ke kokarin shiga ofishin jakadancin Faransar a birnin Yamai.
‘Yan siyasa da jami’an fafutuka a Jamhuriyar Nijar sun fara maida martani bayan da Firai Ministan Gwamnatin rikon kwaryar kasar ya sanar cewa Gwamnatin da soja suka hambarar a watan Yulin da ya gabata ta ci dimbin bashi daga ciki da wajen kasar.
Domin Kari