Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NAKASA BA KASAWA BA: Tarihin Wani Mai Nakasa Shugaban Wata Makarantar Islamiya, Kashi Na 3 - Janairu 24, 2024


Souley Mummuni Barma
Souley Mummuni Barma

A shirin na wannan makon, mun ci gaba ne da ji daga bakin Malan Dalhat Sabi’u Mohammed, shugaban wata makaranta a Kaduna, wadda dagewarsa kan sana’o'in dogaro da kai da maganar neman ilimi suka ba shi damar kai wa matsayin da yake a halin yanzu duk da kasancewarsa mai tawaya a dukkan kafafunsa biyu.

Za mu kuma dora daga inda muka tsaya a baya, Darekta Dalhat ya ci gaba da bayani kan mahimmancin ilimin nakasassu kamar yadda za a ji a karashen tattaunawarsa da wakilin sashen hausa na Muryar Amurka, Isa Lawal Ikara.

Sannan kuma a jamhuriyar Nijar, kungiyoyin masu bukata ta musamman suka dage da aiyukan fadakarwa domin ganar da al’umma tasirin bai wa yaran da ke da tawaya damar samun ilimin zamani.

Wannan yunkuri ya biyo bayan la’akari da yadda, a wasu yankuna, irin su jihar Agadez wasu iyayen ke sakacin da wannan aiki da ke matsayin wani bangare na tarbiyar yara.

Ga kashin farko na hirar wakilin Muryar Amurka Hamid Mahmoud da Abdou Moutsallabi Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Nakasassun jihar Agadez.

Saurari shirin a sauti:

NAKASA BA KASAWA BA: Mahimmancin Ilimin Nakasassu - Janairu 24, 2024
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:58 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG