Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ayarin Karshe Na Sojan Faransa Ya Fice Daga Nijar


Sojojin Faransa
Sojojin Faransa

A yau Juma’a 22 ga watan Disamba ayarin karshe na dakarun Faransa a Nijar ke koma wa gida, sakamakon takun sakar da ke tsakanin kasashen 2,  Faransar ta bada sanarwar rufe ofishin jakadancinta da ke birnin Yamai.

Faransa ta ce ta yi hakan ne saboda abin da ta kira rashin samun cikakken hadin kan da zai bada damar gudanar da ayyuka kamar yadda ya dace.

Gomman sojojin da suka rage daga dakaru 1500 din da kasar Faransa ta kaddamar da aiyukan kwashewa ne suka tashi daga sansanin sojan sama na birnin Yamai a wannan Juma’a don komawa kasarsu kwanaki 9 kenan kafin shudewar wa’adin da hukumomin mulkin sojan Nijar suka bayar don ganin tsofuwar kasar mulkin mallakar ta fice a sanadiyar sabanin da ya biyo bayan juyin mulkin 26 ga watan Yuli.

Sojojin Faransa
Sojojin Faransa

Dama dai tun a zamanin tsohon shugaban kasa Issoufou Mahamadou ‘yan fafutika sun sha nuna rashin amincewa matakin girke sojojin Faransa a Nijar haka kuma suka cigaba da nuna wannan matsayi a zamanin Mohamed Bazoum gwagwarmayar da suka kara zazafawa a washegarin kifar da shi.

Daya daga cikin jagororin gamayyar Front Patriotique Bana Ibrahim ya ayyana ranar ta 22 ga watan Disamba a matsayin wace za a saka a kundin tarihin jamhuriyar Nijar.

Sojojin Faransa
Sojojin Faransa

Sa’oi kadan kafin haka hukumomin Faransa a wata sanarwar da suka fitar dauke da sa hannun korerren jakada Syvain Itte sun ayyana rufe ofishin jakadancin kasar a Nijar tare da sallamar illahirin ma’aikata.

Bana Ibrahim na cewa dama sun san za a yi haka. Ya na mai cewa Nijar ta yi Allah wadai da yarjejeniyar da ke tsakanin kasar da Faransa.

Dangantakar Jamhuriyar Nijar da Faransa wani abu ne da ya samo asali shekaru aru aru inda ko baya ga maganar mulkin mallaka kasashen 2 na da mu’amular cinikayyar karfen uranium da wasu harkokin kamfanoni masu zaman kansu. Raba gari a tsakaninsu a yau abu ne da masana harkokin diflomasiya ke fassarawa a matsayin koma baya kamar yadda Moustapha Abdoulaye masani kan sha’anin diflomasiya ya bayyana.

Sabon abin dangantakar da aka bude a tsakanin Faransa da Nijar wani al’amari ne da masana suka ce dauke yake da darussa da dama da ya zama wajibi hukumomin Faransar su yi la’akari da shi.

Kasar Faransa wace hukumomin sojan Mali suka tilastawa kwashe dakarunta a 2022 ta kafa sansani akan iyakar Nijar haka kuma ta tsallako da wasu daga cikin sojojinta da gwamnatin mulkin sojan Burkina Faso ta kora.

Kin yin na’am da majalissar sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar ya sa a watan Agusta sabbin hukumomin suka tsinke huldar aiyukan soja da Faransa mafarin kwashe wadanan sojoji bayan shafe makwanni da dama na kace nace a tsakanin Janar Tiani da Emmanuel Macron.

Saurari rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:49 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG