Ya na mai cewa ba zai lamunta ba da abinda ya kira shafa kashin kaji saboda haka ya kudiri aniyar maka jakadan a kotu.
A wata rubutacciyar sanarwar da aka aike wa manema labarai, lauyan da ke kare tsohon Shugaban Kasa Issoufou Mahamadou wato Me Illo Issoufou ya fara ne da maida martani kan bayanan bahasin da jakada Sylvain Itte ya gabatar a yayin zaman sirrin da kwamitin tsaron Majalissar Dokokin Faransa ya yi kan abubuwan da ya sani game da juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023.
Lauyan na mai cewa ganawar da jakadan yace sun yi da shi da Tiani da Issoufou, kwanaki 2 bayan juyin mulkin, in dai har an yi ta to kam ba za ta iya zama kwakwarar hujjar da za a zargi Issoufou da hannu a juyin mulkin ba.
Haka kuma Sylvain Itte a ci gaban bahasinsa ya sanar da Majalissar Dokoki cewa abin na da nasaba da sabanin da ke tsakanin Bazoum Mohamed da Ministan Albarkatun Man Fetur, wanda da ne ga Mahamadou Issoufou, dangane da batun nadin mutumin da ya kamata ya shugabanci sabon kamfanin kula da harkokin man fetur, a zaman da majalissar ministoci ta so ta yi a ranar da aka yi juyin mulki.
Sai dai lauyan yace wannan rikici abu ne da Sylvain Itte ya kirkiro domin da Bazoum da Ministan Albarkatun Man Fetur ra’ayinsu 1 akan wancan shiri na harkokin man fetur.
Me Illo Issoufou ya ce jakadan na Faransa ya bayyana wa ‘yan majalissar kasarsa cewa ba su taba tunanin Shugaba Issoufou zai iya ingiza kwamandan dogarawan fadar Shugaban Kasa, wanda mutunensa ne, ya kifar da abokin tafiyarsa na siyasa da suka shafe shekaru 30 tare, zargin da lauyan yace babu kamshin gaskiya hasali ma abu ne da ya ke kallonsa a matsayin yunkurin mayar da Tiani tamkar dan karamin yaron da bai san abin da yake yi ba.
Bayan da ya musanta dukkan zarge-zargen da suka fito a bahasin na jakada Sylvain Itte, lauyan Isssoufou Mahamadou, Me Illo Issoufou ya sake nanata cewa babu hannun tsohon shugaban kasar a juyin mulkin da soja suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum.
Ganin munin kazafin da aka yi masa, Issoufou Mahamadou, ya yanke shawarar shigar da kara a kotu domin a kwatar masa hakkinsa.
Da ma dai tun a washegarin juyin mulkin 26 ga watan yulin 2023 wasu ‘yan Nijar, musamman magoya bayan hambararren Shugaban Kasa, ke zargin Issoufou Mahamadou da hannu a wannan al’amari a bisa wasu hujjojin da suke cewa sun dogara a kansu.
A saurari rahoton Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna