Kungiyar tace wannan wata alama ce da ke fayyace yunkurin yi wa harkokin shai’ar katsalandan saboda haka ta umurci ‘yayanta su fice daga hukumar yaki da cin hanci COLDDEF don kare kansu daga bada gudunmuwa wajen murde wa doka wuya.
Da yake jaddada anniyar yaki da mahandaman dukiyar kasa jim kadan bayan wata ganawa da Janar Abdourahamane Tiani a fadarsa a yammcin juma’a 16 ga watan fabrairu, shugaban hukumar COLDDEF Colonel Abdoul Wahid Djibo ya bayyana cewa, takardun mafi yawancin shari'un din da ‘yan kasa ke jiran ganin an maida hankali kansu na hannun mashara’antu sai dai a dokance hukumar ta sa ba ta da hurumin kula da wadanan takardu dalili kenan za su fara duba hanyoyin da za su bada damar samun sukuni da ikon mayar da wadanan shari'u a hannun COLDDEF ta yadda hukumar za ta gudanar da bincike akan su.
Wadanan kalamai ba su yi wa kungiyar alkalai ta SAMAN dadi ba saboda haka kungiyar ta fitar da sanarwa don mayar da martani kan abinda ta kira yunkurin hada rikici a tsakanin bangaren zartarwa da na shari’a kamar yadda mai shari’a Moussa Mahamadou jigo a kungiyar SAMAN ya bayyana.
Hasali ma wannan al’amari na kama da yunkurin shiga gonar mashara’anta a kasar da aka yi alwashin mutunta yarjeniyoyin kasa da kasa a cewar SAMAN.
A hirar shi da Muryar Amurka, mai shari’a Nani Souley Aboubacar Sidikou, mataimakin babban sakataren kungiyar na kasa ya bayyana cewa, shari'a kadai ce ta ke da hurumin da za ta gurfanar da mutum gabanta domin ta tabbatar da cewa laifin da ake tuhumar shi da shi ya aikata ko bai aikata ba.
Kungiyar ta umurci ‘yayanta su gaggauta ficewa daga hukumar ta COLDDEF don kaucewa bada gudunmuwa wajen yi wa doka karan tsaye.
Korafin na SAMAN na zuwa ne kwana 1 bayan da kungiyar lauyoyin ta Barreau des Avocats ta bayyana damuwa da yadda tace hukumar COLDDEF ta hana lauyoyin gudanar da aikinsu na masu bada kariya ga mutanen da aka kaddamar da bincike kan zarginsu da almundahana, yayin da a daya bangare aka shiga takun saka tsakanin hukumar ta COLDDEF da tsohuwar hukumar yaki da cin hanci HALCIA bayan da COLDDEF din ta zargi jami’anta da lalata wasu bayanan bincike, zargin da tsofaffin ma’aikatan hukumar ta HALCIA suka yi watsi da shi.
Saurari cikakken rahoton:
Dandalin Mu Tattauna