Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Massana Na Karin Haske Akan Ka’idojin Iya Ficewar Kasashe Daga Kungiyar ECOWAS


Kungiyar ECOWAS
Kungiyar ECOWAS

A yayin da hukumomin mulkin sojan Mali, Nijar da Burkina Faso suka bada sanarwar ficewar kasashensu daga CEDEAO sakamakon zargin kungiyar da kauce wa manufofin da aka kakaba, masana na cewa har yanzu akwai sauran sararin warware wannan dambarwa.

NIAMEY, NIGER - Masana dai sun ce akwai wasu ka’idoji dake kunshe a cikin wannan dambarwa da ta biyo bayan juyin mulkin da aka fuskanta a kasashen uku da ke yankin Afrika ta Yamma.

A tattaunawarsa da Muryar Amurka wani lauya da ke aiki a cibiyar nazari da bincike kan dokokin kasa da kasa, Barista Bachir Amadou, mazaunin Montpellier na kasar Faransa, ya bayyana cewa dokokin ECOWAS sun gindaya wasu sharuda da ya zama wajibi kasa ta cika kafin ta fice daga kungiyar.

Hakazalika, Maitre Bachir ya ce abin da wadanan kasashe suka fada tamkar sanarwa ce suka bayar kan shirin su na ficewa daga CEDEAO domin a ka’idar kungiyar, kasa ba ta ficewa kai tsaye, tilas ne a rubuta wa hukumar gudanarwarta don sanar da ita kuma za a jira tsawon shekara guda kafin kudirin ficewar ya tabbata.

Wannan, in ji shi, na iya zama wata damar samar da sulhu ta yadda kasashen za su canza ra’ayi kuma dalili kenan na kayyade tsawon shekara guda.

Lauyan ya kara da cewa lalle ne kungiyar ECOWAS na da hurumin hukunta dukkan wata kasar da aka yi juyin mulki, amma kuma a gaskiya kungiyar ta yi kuskure game da batun Nijar domin babu inda dokokin kungiyar suka bada damar a yi amfani da karfin soja kan sojojin da suka yi juyin mulki.

Idan wadanan kasashe na son ficewa daga CEDEAO, to lallai sai sun bi hanyar da aka shimfida.

Dokokin kungiyar ta ba su yanci amma su bi ka’ida watakila kafin nan da cikar wa’adin shekara guda a na iya samun maslahar wannan dambarwa.

Saurari cikakken hirarasu da wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma:

Karin Haske Akan Ka’idojin Iya Ficewar Kasashe Daga Kungiyar ECOWAS.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:41 0:00

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG