A cikin shirin na wannan makon mun duba halin da malaman ke ciki domin ba ya ga karancin kayan aiki, wadanan malamai na fatan ganin an bullo da hanyoyin ba su horo ta yadda za su sami kwarewar da ke daidai da ci gaban da zamani ya zo da shi don taimakawa daliban.
Taron hukumomi da kungiyoyin kasashen Afrika masu rajin kare hakkin dan Adam karo na 73 da ke gudana a kasar Gambia, ya yaba da yadda jamhuriyar Nijer ta maida hankali wajen mutunta wasu mahimman ‘yancin dan Adam.
Shugabannin hukumar kare hakkin dan adam ta CNDH sun kai ziyara a asibitocin da aka kwantar da mutanen da suka ji rauni a yayin ruwan wutar da jiragen sojan saman Nijar suka yi.
An kafa makarantar ne a wani bangare na matakan shigar da nakasassu a sha’anin ilimin boko ta yadda za su tashi da tunanin rungumar kwakkwarar madogarar rayuwa a maimakon shiga harakar bara.
Hukumomin Nijer sun fara nazarin sabbin hanyoyin magance matsalar bara bayan la’akari da yadda wasu ‘yan kasar dauke da yara kanana ke kwarara zuwa kasashen waje da nufin rungumar wannan kaskantacciyar sana'a duk da jan hankalin da hukumomi da kungiyoyi ke yi.
Gwamnatin Jamhuriyar Nijer da Kungiyar Tarayyar Turai sun saka hannu akan wata yarjejeniya wace a karkashinta kungiyar EU ta amince ta ba kasar ta Nijer tallafin biliyan kusan 10 na kudaden cfa wadanda za a yi amfani da su don bunkasa sha’anin ilimi.
Fitaccen dan siyasa a Jamhuriyar Nijar Doudou Rahama na hannun daman tsohon shugaban kasa Mahaman Ousman da magoya bayansa ,sun bada sanarwar canza sheka daga jam’iyar RDR Canji zuwa PNDS Tarayya ta shugaba Mohamed Bazoum.
Ma’aikatar tsaron Nijer ta sanar cewa wasu jiragen sojan kasar sun hallaka ‘yan ta’adda a wata mahakar zinare da ke kauyen Tamou na gundumar Say a jihar Tilabery, sai dai wasu ‘yan rajin kare hakkin bil'adama na ganin akwai bukatar a gudanar da bincike don gano zahirin abinda ya faru.
Magoya bayan jam’iyar Moden Lumana ta tsohon Firai Minista Hama Amadou sun gudanar da babban taro domin bitar halin da jam’iyar ke ciki.
Shugaban kungiyar fafutuka ta Tounrons La Page Internatinale ya jaddada aniyar ci gaba da gwagwarmayar kare muradun kasashen Afirka bayan da ofishin jakadancin Faransa a birnin Yamai ya bada sanarwar soke takardar bizar da ke bashi izinin shiga kasar ta Faransa.
Wasu kungiyoyin fafutika na hadakar M62 a Jamhuriyar Nijer sun kudiri aniyar gudanar da zanga zangar lumana a ranar 30 ga watan nan na Oktoba da nufin tada hukumomi daga barci dangane da wasu tarin matsalolin da suka addabi jama’a.
A Nijer, hadakar kungiyoyin fafutikar M62 sun kudiri aniyar gudanar da zanga-zangar lumana a ranar 30 ga watan Oktoba don tada hukumomi daga barci a kan matsalolin da suka addabi jama’a ciki har da sha’anin tsaro, lamarin da ke nuna rashin tasirin girke rundunar sojojin Faransa a kasar.
Wata ‘yar majalissar dokokin kasa daga bangaren masu rinjaye a Jamhuriyar Nijar, ta shawarci takwarorinta ‘yan majalissa da ma hukumomi akan bukatar nazarin hanyoyin warware sarkakiyar dake tattare da dokokin kasar game da batun mu’amular mutane masu jinsi daya.
Jam’iyar hamayya ta ADR Mahita a Jamhuiriyar Nijar ta bayyana damuwa dangane da abinda ta kira halin kuncin rayuwar da jama’ar kasar ke ciki sanadiyar wasu tarin matsaloli da suka hada da lalacewar lamuran tsaro da durkushewar tattalin arziki, ilimi da kiwon lafiya.
Gwamnatin jamhuriyar Nijer ta jaddada aniyar soma zartar da tsarin inshorar manoma a shekarar 2023 da nufin takaita dimbin asarar da bala’in ambaliya da sauran illolin canjin yanayi ke haddasa wa manoma, makiyaya da masintan kasar a wannan lokaci da tallafin masu hannu da shuni ke karanci.
Hukumomin jamhuriyar Nijer sun bada sanarwar rufe wasu makarantu masu zaman kansu dake horar da likitoci saboda zarginsu da rashin cika wasu mahimman ka’idodin da suka shafi sha’aniin kiwon lafiya.
Kungiyar kare hakkin jama’a da bunkasa dmokradiya a Jamhuriyar Nijar ta shirya wata mahawara a bainar jama’a da ta hada bangarorin siyasar kasar domin tantauna halin da ake ciki .
Ministan kudin Nijer ya sanar cewa kasar ta fuskanci cikas wajen aiwatar da kasafin kudin shekarar 2022, lamarin da ake alakantawa da matsalolin tsaro, illolin yakin Rasha a Ukraine. Lura da wannan ya sa gwamnatin ta Nijer maida hankali akan maganar tattara kudaden harajin cikin gida a kasafin badi.
Mun samu bakuncin wani makaho da ya shahara a wani fannin da ba kasafai ake samun masu lalurar indanu cikinta ba.
Domin Kari