Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Jami’an Bankin Tallafawa Manoma Da Makiyayan Nijer 16 Kan Wata Badakala


Manoma a Nijer
Manoma a Nijer

Hukumomi a jamhuriyar Nijer sun cafke wasu manyan jami’an bankin Manoma na BAGRI, saboda zargin rubda ciki akan dubban miliyoyin CFA matakin da ya dauki hankalin kungiyoyin manoma da na jami’an yaki da cin hanci.

Yayin da wasu ke nuna dari dari akan yiwuwar hukunta wadanan jami’ai, wasu kuwa sun fara tunatar da shugaban Nijer Mohamed Bazoum, alwashin da ya sha a ranar da ya yi rantsuwar kama aiki.

A karshen makon jiya ne hukumar ‘yan sandan farin kaya ta cafke jami’an bankin BAGRI su kimanin 16, ciki har da darektoci don yin bayani kan wata almundahana da ta shafi kudaden da aka kiyasta sun haura million 5000 na CFA.

Wannan kokari ya janyo hankula da amincewar al’umomi da kungiyyoyin fararen hula a fadin jamhuriyar Nijer. Mai taimakawa shugaban gamayyar kungiyoyin Manoma da Makiyaya ta Plate Forme Paysanne Abdou Nino Gajango, ya bayyana gamsuwa da wannan mataki.

Reshen kungiyar Transparency International ta hanyar shugaban kungiyar a Nijer Malan Maman Wada, ta ce ta na bin diddigin wannan badakala wace a fili ke tabbatar da cewa cin hanci ya yadu a kowane fanni a Nijer.

Rahotannin baya bayan nan sun yi nuni da cewa an sallami wasu 8 daga cikin jami’ai 16 bayan sauraren bahasinsu, a ofishin ‘yan sandan PJ yayin da ake saran gurfanar da 8 din da suka yi saura a gaban alkali.

A daya bangaren kuma, wasu ‘yan kasa na nuna damuwa akan abin da ka iya zama matakin karshe a wannan badakala dake fayyace yadda ‘yan boko ke ci da gumin mazauna karkara.

Wannan ya sa reshen kungiyar Transperncy ke tunatar da shugaban kasa Mohamed Bazoum alkawarin da ya yi wa al’umma a ranar da yake rantsuwa akan alkur’ani a gaban tarin mutane.

A shekarar 2009 ne tsohon shugaban kasa Tandja Mamadou, ya assasa shirin kafa bankin BAGRI da nufin taimaka wa Manoma da Makiyaya, sai dai tun daga lokacin aiyukan banki a 2010 fara tafiyar hawainiya abin da ya sa a shekarar 2022, kungiyoyin Manoma da Makiyaya suka kudiri sayen babban kaso na hannun jarin bankin, don kubutar da shi.

Domin karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00

Zaben 2023

TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Tasirin Da Zaben Donald Trump Zai Yi A Harkokin Kasashen Duniya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG