NIAMEY, NIGER - Sun kwatanta mutuwar mutumin da ake yi wa lakabi da sarkin ‘yan kwallon duniya a matsayin wani babban rashi a duniyar wasanni.
Edson Arentes Do Nascimento da aka fi sani da sunan Pele wanda ya rasu ranar Alhamis a wani asibitin Sao Polo na kasar Brazil shi ne dan kwallo mafi samun daukaka a fadin duniya sakamakon bajinta da kwarewarsa a harakar kwallon kafa.
Yadda rasuwar wannan taliki ta girgiza duniya haka abin yake a nan Nijar inda wasu ‘yan kasar suka bayyana alhini.
Pele wanda ya rasu ya na da shekaru 82 a duniya ya zura kwallo 1282 a tsawon shekarun da ya shafe ya na taka rawa. Shi ne wanda kawo yanzu dan wasa daya tilo da ya taba samar wa kasarsa kofin kwallon duniya sau 3.
Dan jarida dake bin diddigin sha’anin wasannin motsa jiki Moussa Kambay Garba ya bayyana marigayin a matsayin wanda ya taka rawa wajen cusa sha’awar kwallon kafa a zukatan jama’ar sassan duniya.
Hukumar kwallon kafar Nijar, Fenifoot a ta bakin mataimakin shugabanta Alhaji Sani Otis ta bayyana kaduwa da abinda ta kira babban rashi. A yanzu haka hukumar na dab da tura sakon ta’azziya ga takwararta a kasar Brazil.
Tuni aka ayyana zaman makoki na tsawon kwanaki 3 domin nuna juyayin rasuwar Pele.
An kuma sanar cewa a ranar Litinin din da ke tafe ne za a yi jana’izar Pele da karbar ta’azziya a hukunce inda za a ajiye gawarsa a filin kwallon kafar Santos FC wato kungiyar da ya buga wa kwallo daga 1956 zuwa 1974. Sannan a ranar Talata za a zagaya da gawarsa a titunan birnin Santos.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma: