Tuni aka kafa kwamiti domin gudanar da bincike don gano dalilan faruwar wannan hatsari.
A wata sanarwar da ta fitar a jiya litinin da rana ne ma’aikatar tsaron kasa tace wani jjirgin soja mai saukar angulu samfarin MI 17 ya fadi kuma kuma da wuta lokacin da yake kokarin safka a filin jirgin sojan sama dake birnin yamai.
Dukkan wani yukurin kashe gobarar ya ci tura lamarin da ya haddasa mutuwar sojojin kasar 2 da wani sojan kasar waje 1 abinda ya jefa zullumi a zukatan ‘yan kasa irinsu AbdoulRazak Ibrahim da Rafiou Abba Dan Illela.
Sanarwar hukumomin tace tuni aka kafa kwamiti domin gudanar da binciken da zai bada damar gano mafarin wannan hatsari matakin da jami’in fafutika na gamayyar FSCN Abdou Idi ya yi na’am da shi.
Jama’a na bayyana fatan ganin an maida hankali a wannan aiki ta yadda za a gaggauta sanar da ‘yan kasa zahirin abubuwan da suka yi sanadin faruwar wannan hatsari.
Ministan tsaron kasa a wannan sanarwa amadadin babban kwamandan kwamandojin Nijar wato shugaban kasa Mohamed Bazoum ya isar da sakon alhini zuwa ga rundunar mayakan kasa da ma baki dayan al’umma sakamakon rasuwar wadanan barade da hatsarin jirgi ya rutsa da su jim kadan bayan sun fito daga atisaye.
Saurari rahoton: