Majalisar Dinkin Duniya ta ware duk ranar 15 ga watan Mayu a matsayin ranar karrama rayuwar iyali a fadin Duniya, taken bukin na bana ya shafi maganar ilimi da tattaunawa don zaman lafiya a gidaje.
Gwamnatin Jihar Neja ta shirya taron bita ga manyan malaman jihar akan muhinmancin kaucewa furta kalaman tada hankalin jama’a a lokutan wa’azin watan Ramadan mai zuwa.
Yanzu haka an fara cece-kuce a jihar Adamawa game da batun sauya sheka da ake cewa wasu kusoshin jam’iyar PDP a jihar sun yi zuwa jam’iyar APC, batun da su ‘yan PDP ke cewa cewa wannan batu ba gaskiya bane.
A jiya Alhamis ne jami’an hukumar shige da ficen Amurka suka ce sun kawo karshen farautar ‘yan Daba da su ka kwashe makonni shida su na yi, inda suka kame kusan mutane 1100 wanda suke mambobin wasu munanan kungiyoyi.
A jiya Alhamis ne wani jami’in tsaron ‘kasa na Amurka, ya fadawa ‘yan Majalisa cewa Amurka ta sanar da jami’an Faransa cewa Rasha ta yiwa hanyar sadarwar kwamfutocin Faransa kutse lokacin da ake gudanar da zaben shugaban ‘kasa, tun kafin kowa ya sani.
A jiya Alhamis ne shugaban Amurka Donald Trump ya fito ‘karara ya fadi cewa a baya ya tambayi shugaban hukumar bincike ta FBI kan cewa ko ana gudanar da bincike akansa.
A yau Juma’a za a dawo da sauraron shari’ar tsohon ministan Abuja Sanata Bala Mohammad, gaban kotun birnin tarayya wadda ta tura shi zaman wakafi a gidan yarin Kuje.
Tsohon gwamnnan jihar Sokoto, Attahiru Dalahatu Bafarawa, ya ce ‘daukar sabbin matakai kan mai martaba sarkin Kano Sanusi bayan sulhu da gwamnoni suka yi kan lamarin a Kaduna ba dai-dai ba ne.
Gwamnan jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello, ya ce kungiyoyin addinai na da rawar takawa a yaki da cin hanci a Najeriya.
Wani jirgin ruwan jami’an kiyaye gabar tekun Libya ya kwashe wasu bakin haure 350 a kan teku a jiya Laraba, bayan wata zazzafar arangama da wani jirgin ruwan Jamus mai shawagi kan teku wanda ka iya kai ga mutuwa.
Shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan ya ce zasu sa kafar wando daya da shugaba Donald Trump, game da shawarar da Amurka ta dauka na ba mayakan Kurdawa kayan yaki, idan suka hadu a nan Washington a mako mai zuwa.
Shugaban Amurka Donald Trump ya kare kansa game da matakin da ya dauka na sallamar daraktan hukumar bincike ta FBI James Comey, yana cewa, “Ai baya aikinsa ne da kyau. Illa iyaka”
Majalisar dokoki ta jihar Kano ta kafa kwaitin bincike akan mai martaba Sarkin Kano da majalisar Masararutar Kano, game da zargin kashe kudade ba tare da amincewar ita majalisar ba.
Rundunar ‘Yan Sandan jihar Taraba ta kama wani mutum daya kashe wani yaro karami ya kuma sara shi gunduwa –gunduwa.
Shugaban Amurka Donald Trump ya sallami shugaban Hukumar Bincike ta FBI, James Comey.
Shugaban Sudan Ta Kudu Salva Kiir ya sallami dadadden Hafsan Sojojin Kasar Paul Malong.
A kalla mutane 13 sun rasa rayukansu jiya Talata, bayan barkewar fada tsakanin sojojin gwamnati da mayakan ‘yan ta’adda a kudu maso yammacin Somalia, a cewar shaidu da kuma jami’ai.
Noma Tushen Arziki
Majalisar Dinkin Duniya MDD ta ce tana marhaban da kubutar da yan mata 82 na makarantar Chibok da yan ta’addar Boko Haram suka yi garkuwa dasu a Najeriya, kuma ta yi kira ga iyalai da jama’a da a taimakawa wadannan yan mata da suke cikin dimuwa.
Gidauniyar tallafawa jihohin arewa maso gabas da gwamnatin jihar Adamawa, sun saka hanu kan yarjejeniyar aiki kafada da kafada ta naira miliyan arba'in don sake gina asibitocin Michika da Mubi.
Domin Kari