Erdogan ya fada a jiya Laraba cewar, a wannan yakin da ake yi da IS da ake kiranta Daesh a Larabce, ba daidai a bar wata kungiyar ta’addanci ta yi. Yace wannan matakin zai iya jefa Syria da yankin baki daya cikin hadari.
Mayakan Kurdawa na kungiyar YPG sune masu dakaru kwararrun a yakin da ake yi da kungiyar IS a Syria.
Sai dai Turkiya tana ganin mayakan nada alaka da Kungiyar Ma’aikatan Kurdawa ta PKK mai adawa da gwamnatin Turkiyar. Turkiya da Amurka sun ayyana kungiyar PKK kungiyar ta’addanci.
Ministan harkokin wajen Turkiya Mevlut Cavusoglu yace duk wani makamai da kungiyar mayakan Kurdawan ta YPG zata samu barazana ce ga Turkiya.
Shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan ya ce zasu sa kafar wando daya da shugaba Donald Trump, game da shawarar da Amurka ta dauka na ba mayakan Kurdawa kayan yaki, idan suka hadu a nan Washington a mako mai zuwa.
WASHINGTON D.C. —
Facebook Forum