Wannan ya biyo bayan ajiye aiki da Janar-Janar da dama su ka yi, wadanda su ka yi zargin cewa Sojojin Sudan Ta Kudu sun aikata kisan kare dangi da kuma laifukan yaki. Ba a san ko za a nada Malong kan wani mukami ne na dabam ba.
Shugaban kasar ya nada James Ajong a matsayin sabon Hafsan sojin kasar. Wani dan takaitaccen umurnin soji da aka yada ta kafar talabijin na gwamnati bai yi bayanin dalilin Shugaba Kiir na daukar wannan mataki na maye Malong da wani ba.
Sudan Ta Kudu ta fada yaki ne tun bayan da aka shiga kokuwa kan mukami a 2013 tsakanin Kiir dan Kabilar Dinka da Mataimakinsa, Riek Machar, dan Kabilar Nuer. Wannan gwagwarmaya ta rikide zuwa yaki gadan-gadan a Juba babban birnin kasar, wanda nan da nan ya wanzu zuwa sassan Kasar.
Wannan tashin hankalin ya haddasa karancin abinci a sassan kasar baya ga tsadar abinci da kuma rashin sauran harkokin yau da gobe. Sannan yakin ya tilasta mutane a kalla miliyan 3 barin gidajensu.
Facebook Forum