A wata wasika mai gautsi da ya rubuta ma Comey jiya Talata, Shugaba Donald Trump ya gaya masa cewa, "A halin yanzu an sauke ka, an kuma raba ka da aiki ba tare da bata lokaci ba." Shugaba Trump ya kara da cewa Comey "ya kasa jagorantar wannan ofishin yadda ya kamata."
Akan nada Shugabannin FBI ne su yi wa'adi daya, na tsawon shekaru 10. Shi kuwa Comey shekaru 4 da su ka gabata aka nada shi.
Ya na California ne lokacin da wani hadiminsa ya shaida masa cewa an fa sallame shi. Zuwa yanzu bai ce komai ba ga jama'a.
An bayyana dalilan sallamar Comey a wasu wasiku biyu da Attoni-Janar Jeff Session da Mataimakinsa Rod Rosenstein su ka rubuta. A takaice dai su na arginsa ne da rashin bin doka da ka'ida.
Comey ya "aikata laifuka masu tsanani" game da yadda ya kammala binciken yadda abokiyar karawar Trump a zaben shugaban kasa Hillary Clinton ta yi da sakonnin email, a cewar Rosentein, ya na mai zargin Shugaban FBI da shan gaban Attoni-Janar ta wajen cewa ba za a gurfanar da tsohuwar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka gaban shari'a ba.
Shugaban Amurka Donald Trump ya sallami shugaban Hukumar Bincike ta FBI, James Comey.
WASHINGTON D.C. —
Labarai masu alaka
Nuwamba 09, 2024
Facebook Forum