Mataimakin gwamnan jihar Neja, Ahmed Muhammad Ketso, wanda ya kasance a taron bitar, yace gwamna ya amince da taron bitar ne domin malamai su sami jituwa bakinsu ya zamanto ‘daya, kuma suna bisa koyarwar kur’ani mai girma da hadisi.
Babban daraktan kula da harkokin addinai na jihar Neja, Alhaji Umar Faruk Abdullahi, ya ce sun shirya taron bitar ne bisa la’akari da zamani, kasancewar yadda rigingimu ke ‘kara ‘karuwa ta hanyar addini. Hakan yasa gwamnatin jihar Neja ke kokarin rufe duk hanyoyin da rigima za ta iya fitowa.
Wasu daga cikin manyan malaman da suka halarci wannan taro sun nuna jin dadinsu da kuma cewa yin hakan yana kawo hadin kai ga al’umma domin ya hada kan musulmai a guri ‘daya don fahimtar juna.
Duk da wannan mataki da gwamnatin Neja ta dauka, wasu manyan malamai Islama a Najeriya na ganin akwai bukatar sanya idanu ga ‘daliban Najeriya masu zuwa neman ilimi a kasashen Larabawa domin tabbatar da ganin basu fada cikin kungiyoyin ta’addanci ba, kamar yadda shugaban kungiyar Izala Shiekh Abdullahi Bala Lau ya fada.
Facebook Forum