An bayyana muhimmancin kungiyoyin addinai wajen taimakawa gwamnatin Najeriya a kokarinta na yaki da cin hanci da rashawa a kasar.
Kokarin kawar da cin hanci da rashawa a Najeriya na ‘daya daga cikin alkawuran da gwamnatin APC ta yiwa ‘yan kasar. gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya ce idan har kungiyoyin addinai da malamai suka dukufa wajen fadakarda jami’an gwamnati, zai yi tasiri kuma zai taimakawa gwamnati.
Gwamnan ya fadi haka ne alokacin da yake jawabi bayan da ya karbi bakuncin tawagar shugabannin kungiyar Izala na Najeriya.
Shugaban kungiyar Izala a Najeriya, Sheik Abdullahi Bala Lau, ya ce sun kai ziyarar ne jihar Neja a ci gaba da ziyarar da suke a jihohin Najeriya, domin duba ayyukan kungiyar na fadakar da al’umma a matakin jihohi. Sannan kuma da ganawa da shugabannin jama’a domin fadakar da su muhimmancin yin adalci.
Zagayen na kungiyar Izala dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da hukumomin Najeriya ke ‘kara matsa ‘kaimi wajen bankado mutanen da suka yi almundahana da dukiyar gwamnati, al’amarin da ke shan yabo daga masu fafutukar ganin an kawai da cin hanci a tsakanin al’umma.
Domin karin bayani saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari.
Facebook Forum