'Yan kwanakai kadan gabanin fara azumin watan ramadan na bana, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jagoranci gagarumin taron bude babban masallacin JIBWIS a helkwatar kungiyar da ke Abuja.
Karshe dai tsohon gwamnan jihar Nassarawa, Abdullahi Adamu da akasarin ‘yan takara a babban taron jam’iyyar APC, sun samu nasara ta hanyar daidaitawa, ba tare da kada kuri’a ko daya ba.
Tsohon gwamnan Jihar Zamfara Abdul'aziz Yari ya ce har yanzu ya na cikin takarar neman shugabancin APC duk da batun tura kujerar arewa ta tsakiya.
Babbar jam’iyyar adawar Najeriya PDP na fara sayar da fom din takarar shugaban kasa, magoya bayan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na kan gaba wajen sayan fom din.
Jam'iyyar APC ta fitar da sanarwar kudin sayan fom Naira miliyan 20 don takarar shugaba da kuma na mataimakin shugaban jam'iyyar Naira miliyan 10. Duk sauran mukamai Naira miliyan 5.
Matasa da su ka yi gwagwarmayar amincewa da dokar rage shekarun tsayawa takara, sun jaddada fatar cewa shugaba Buhari zai cika mu su alkawarin da ya yi a lokacin sanya hannu kan dokar na mika mu su ragamar mulki a 2023.
Alamu na nuna an samu rabuwar kawuna a tsakanin gwamnonin jam’iyayr APC 23 gabanin babban taron jam’iyyar a 26 ga watan nan.
Masu ruwa da tsaki na lamuran masana’antu da kasuwanci a Najeriya sun taru a Abuja don kaddamar da tambarin bude tashar sauke hajar teku ta Kano da ke Dala mai taken tashar “TSANDAURI”
Jirgi na uku dauke da ‘yan Najeriya da ke ficewa daga Ukraine don tsira daga mamayar Rasha, ya isa filin saukar jiragen sama na Abuja.
Kamfanin jirgin sama na MAX ya ba da labarin tashin jirgin sa daya zuwa birnin Bucharest na kasar Romania don kwaso daliban Najeriya da su ka makale a can sanadiyyar mamaye Ukraine da kasar Rasha ta yi.
Masana siyasa na cewa bayan babban taron APC a watan gobe, za a samu karin manyan ‘yan siyasa da za su kafa jam’iyya ta uku mafi karfi da Sanata Rabi’u Kwankwaso ya shimfidawa tabarma.
Barazanar gagarumar zanga-zangar ta kungiyar daliban Najeriya a litinin din nan, ya jawo kira daga wasu iyaye da masu ruwa da tsaki na sara da duba bakin gatari.
masana kimiyyar siyasa da masu sharhi na cewa akwai sauran rina a kaba, bayan sanya hannu da shugaba Buhari ya yi kan sabuwar dokar zabe.
Tuni wannan matakin ya zaburar da wata kungiya mai da’awar sulhu ta APC a Kano karkashin Alh.Yusuf Ado Kibiya da ke shirin sulhunta bangaren gwamna Ganduje da na sanata Shekarau da zummar dakatar da tasirin sabuwar tafiyar.
A ranar 26 ga watan nan na Fabrairu jam'iyyar mai mulki ta APC za ta gudanar da taron nata.
Kungiyoyin matasa magoya bayan jam’iyyar APC sun juya taron rantsar da shugabannin jam’iyyar na jihohi zuwa dandalin kamfen din amsar madafun ikon jam’iyyar.
Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da tsohon gwamnan Imo Sanata Rochas Okorocha sun bayyana niyyar su ta yin takarar shugabancin Najeriya a zaben 2023
Yayin da masu sha’awar takarar shugabancin Najeriya a badi ke kara bayyana muradin su, tsohon shugaban zauren jam’iyyu Yunusa Tanko ya ce za a iya samun garambawul ga tsarin shugabancin Najeriya.
Domin Kari