Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Jagoranci Bude Masallacin Helkwatar Izala A Abuja


Bude Masallacin Izala
Bude Masallacin Izala

'Yan kwanakai kadan gabanin fara azumin watan ramadan na bana, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jagoranci gagarumin taron bude babban masallacin JIBWIS a helkwatar kungiyar da ke Abuja.

A matsayin babban bako a wajen bude masallacin, shugaba Buhari ya ayyana bude masallacin don fara sallah a cikin sa da sauran ayyukan ibada.

A lokacin bude masallacin, shugaban JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau ya jagoranci sallar jumma’a inda ya yi huduba da yin addu’a ga samun zaman lafiya mai dorewa a Najeriya.

Sheikh Bala Lau wanda ya kawo tarihin gina masallacin daga gudunmawar fatun laiya da tallafin wasu bayin Allah, ya yi addu’ar rahama ga daya daga wadanda su ka tallafa ya kuma bayyana sunan sa don Allah ya yi ma sa rasuwa wato Magajin Garin Sokoto Alhaji Hassan Danbaba.

Shehun malamin ya bukaci shugaba Buhari ya duba kara tallafawa jama’a musamman talakawa da kayan abinci don yanda a ke fama da tsadar rayuwa.

Shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan, wasu gwamnoni da su ka hada Babagana Zulum, Umar Fintiri da Atiku Bagudu, Sanata Danjuma Goje da sauran ‘yan majalisar dattawa da shugaban kamfanin NNPC Mele Kyari Kolo da sauran jama’a da dama sun shaida bude masallacin.

Ga Nasiru Adamu El Hikaya da karin bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00

XS
SM
MD
LG