A wannan karo, fiye da wani lokaci a baya, matasa sun fito don takarar mukaman jam’iyyar a babban taron da za a gudanar a ranar 26 ga watan nan na Fabrairu.
Taron dai wanda ya gudana duk da ba a rantsar da dukkan shugabannin ba saboda rashin warware takaddama ko shari’a, ya janyo dimbin ‘yan jam’iyyar daga sassan kasar wadanda su ka rika daga hotunan gwanayen su da su ke son musamman su zama shugabannin jam’iyyar.
Matasa da mata sun fi cinye kasuwar don yanda su ka wuni su na rausayawa a bakin kofar shiga sakatariyar jam’iyyar.
Shugaban hadakar matasan jam’iyyar Adamu Dahiru Lanzai ya jagoranci taron manema labaru a gefen taron inda a ra’ayin sa lauya daga Taraba Barista Muhammad Bello Mustapha ya cancanci shugabancin jam’iyyar.
A na sa bangaren mai son takarar matasa na jam’iyyar daga Filato Barista Munka’ila Yahaya Mabu ya ce da matasan sun tsaya a kujerar matasan don gyara dabi’un matasan da ya ke da ra’ayin akasarin su masu kasala ne.
Shi kuma dan takarar mukamin matasa daga Jigawa Ahmad Abba Dangata ya ja hankalin matasan ne wajen kaucewa zama ‘yan amshin shatan manyan ‘yan siyasa da ba su faye damuwa da kadun matasan ba, bayan darewa madafun iko.
Tun hawa kujerar mafi karancin shekaru a matasa Muhammad Kadade a matsayin shugaban matasan jam’iyyar adawa ta PDP, matasa ke kara yunkurowa a manyan jam’iyyun biyu don takarar mukaman jam’iyya da na gwamnati.
Saurari rahoto cikin sauti daga Nasir Adamu El-Hikaya: