Labarin ikirarin tsige Mai Mala Buni din ya nuna cewa umurnin hakan ya fito ne daga shugaba Buhari, amma nan take jami’an jam’iyyar su ka ce labarin ba gaskiya ba ne.
Duk da bayyanar gwamnan Neja Abubakar Sani Bello a helkwatar jam’iyyar bai hana labaru masu cin karo da juna ba, da jami’an jam’iyyar ke cewa gwamnonin da su ka taru duk na goyon bayan Mai Mala Buni, kuma ‘yar hatsaniyar ta shafi zaben shiyyoyi na jam’iyyar ne.
Babban jami’in yada labarun jam’iyyar, Salisu Na Inna Dambatta, ya ce Mai Mala na kan kujerarsa.
Na tambayi gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje kan labarin inda ya ce a waje na ne ma ya samu labarin.
Koma dai me ya faru, Sanata Kabiru Gaya ya ce Mai Mala ya yi bakin kokarin rikon jam’iyyar.
A yanzu haka Mai Mala Buni ya na ketare don haka za a jira karin bayanai a yayin da jam’iyyar ta ayyana 26 ga watan nan a matsayin ranar babban taro.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: