Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya jagoranci taron manyan abokansa a siyasa daga dukkan sassan Najeriya wajen kaddamar da wata kungiyar siyasa.
Muradun kungiyar a jawaban da a ka gabatar na nuna kalubalantar manyan jam’iyyun siyasa biyu na APC da PDP a babban zaben 2023 mai zuwa.
Taron wanda ya samu halartar ‘yan siyasa da dama da su ka hada da tsoffin gwamnoni da ministoci har da tsoffin ‘yan siyasa irin Tanko Yakasai, na nuna lokacin sabon canji ya yi, bayan wanda jam’iyyun adawa su ka yi nasarar yi a 2015 bayan gwagwarmayar shekaru 12.
Injiniya Buba Galadima da ke kan gaba a taron ya tabbatar da a karshe su ka iya neman rejistar su zama jam’iyya ko narkewa cikin wata jam’iyyar.
Tuni wannan matakin ya zaburar da wata kungiya mai da’awar sulhu ta APC a Kano karkashin Alh.Yusuf Ado Kibiya da ke shirin sulhunta bangaren gwamna Ganduje da na sanata Shekarau da zummar dakatar da tasirin sabuwar tafiyar.
Farfesa Mukhtari Banana shi ne sakataren kungiyar maslahar da ke cewa ya na da muhimmanci a daure tsuntsiyar APC da igiya daya a Kano.
Shaharerren mai shirin silima na Kannywood Hamisu Lamido Iyan Tama ne jami’in labarun tafiyar da shi ma ya ke cewa za su yi duk abun da ya dace don gudun fafa-gora ranar tafiya, kasancewar karfin Sanata Kwankwaso na Kano.
Za a jira a ga yanda sabuwar tafiyar Kwankwaso mai taken “The National Movement” za ta gudana daidai lokacin da a ke kara fahimtar alkiblar manyan jam’iyyu don tinkarar babban zaben.
Sauraren cikakken rahoton Nasiru Adamu El Hikaya daga Abuja: