Shugaban dai ya bukaci matasan su mara ma sa baya ya zarce a zaben 2019, in ya so 2023 zai zama matasa ne za su dare madafun iko.
A wani gagarumin taro a Abuja, dan rajin kare muradun matasan Hamzat B Lawal ya ce suna kyautatawa shugaba Buhari zato cewa zai cika wannan muradin gadar da kujera ga sabbin jini.
Lawan wanda ya gayyaci matasa da shugaban kungiyoyi daga sassan Najeriya, ya ce duk da sanin wannan alwashi, amma matasan ba za su jira sai an mika mu su mulki ba, za su karade kasa da kamfen din shawo kan matasa miliyan 40.
Tsohuwar kansila a Abuja Zainab Buba Galadima da ta halarci taron, ta ce in matasan sun shirya da gaske za su iya samun nasara.
Shugaban wata kungiya mai rajin gaskiya da amana CITAI a takaice da ke Maiduguri Abubakar Sadiq Mu’azu ya ce ba lalle sai duk matasa sun yi takara ba, za su iya marawa tafiyar ‘yan uwan su don cimma muradi.
Zuwa yanzu a duk cikin wadanda ke kan gaba a aniyar takarar 2023 dattawa ne kuma ba alamar manyan jam’iyyu za su mika tikitin su ga matasa ‘yan kasa da shekaru 50.
Ga dai rahoton Nasiru Adam El Hikaya daga Abuja: