Sabon sarkin Alhaji Ahmed Garba Gunna, ya nemi hadin kan al’ummar masarautar wajen shawo kan babbar matsalar da ke ci wa masarautar tuwo a kwarya, wacce ta shafi rashin zaman lafiya.
‘Yan sanda a jihar Neja sun ce suna bincike kan wani matashi dan kimanin shekara 20 mai suna Lawali Danladi da ake zargin ya kashe matarsa.
Rahotanni sun ce kotun ta tura su gidan yarin ne don su yi zaman jira, gabanin ta karbi shawarwari daga ma’aikatar shari’ah ta jihar Nejan.
Rundunar 'yan sandan jihar Neja Najeriya ta ce tana bincike akan wata mata 'yar kimanin Shekara 24 mai suna Amina Aliyu bisa zargin yi wa kishiyarta kisan gilla a unguwar Tunga da ke cikin fadar gwamnatin jihar ta Neja.
Shugabannin addinai a jihar Kwara da ke Najeriya sun bukaci a kwantar da hankali bayan barkewar rikicin sanya hijabi da ya faru a wata makarantar sakanadare da ke birnin Ilori, har mutane 5 suka jikkata.
Ganin yadda sace dalibai ke neman zama yayi a arewacin Najeriya, gwamnatin jihar Neja ta rufe makarantun sakandarenta har na tsawon makwanni biyu don nazarin al'amarin
Al’ummar masarautar Kagara a jihar Nejan Najeriya na ci gaba da zaman jiran sabon sarkinsu bayan rasuwar tsohon sarkin Mai Martaba Alh. Salihu Tanko a cikin makon da ya gabata
Gwamnatin jihar Nejan Najeriya ta sanar da rasuwar Sarkin Kagara mai daraja ta daya mai martaba Alhaji Salihu Tanko da yammacin ranar Talata.
Masana da masu ruwa da tsaki a fannin harkokin kasuwanci da tattalin arziki a ciki da wajen Najeriya na ci gaba da ba shugabar kungiyar kasuwanci ta duniya, Ngozi Okonjo-Iwela shawarwari a kan yanda zata taimaka wa kasashen Afrika wurin yin cinikayya da sauran kasashen duniya.
Wasu ‘yan bindiga dauke da manyan bindigogi sun sake kai wani sabon hari da ya hallaka mutum akalla 6 a jihar Neja da ke arewacin Najeriya.
Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta ce ta amince da yi sulhu da ‘yan bindiga idan har hakan zai taimaka wajen magance matsalar hare haren ‘yan bidigar da suka addabi musamman yankin Arewacin kasar.
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya kyankyasa inda yake ganin masu garkuwa da mutane suka boye daliban makarantar Kwalejin Kimiyya ta Kagara da ke jihar Neja.
A kalla mutum hudu ne wasu yan bindiga suka kashe tare da yin awon gaba da wasu mutum 10, a kauyen Akufe na gundumar Kuchi a karamar hukumar Sarkin Pawa a jihar Neja ta Najeriya.
A daidai lokacin da ake ci gaba da zama cikin zullumi tare da neman hanyar ceto daliban Kagara da aka sace, wasu daga cikin daliban da suka tsallake rijiya da baya sun bayyana halin da suka shiga
'Yan bindiga sun kai wani sabon hari da ya yi sanadin mutuwar mutane 21 a jihar Naija.
Yayin da ake ci gaba da samun matsalolin tsaro a Najeriya, an shiga zarge zargen juna tsakanin masu ruwa da tsaki.
Duk da gayyato 'yan sandan kwantar da tarzoma na mobayil, wannan bai hana barayin shanu arcewa da shanun ba. Hasali ma, sai da su ka kashe daya daga cikin 'yan sandan, su ka kuma raunata guda.
Wasu mahara dauke da manyan bindigogi akan babura sun yi awon gaba da wasu mutane kimani 15 a jihar Neja da ke Arewacin Najeriya.
Matsalar Tsaro na kara ta'azzara a sassan Najeriya musamman a arewacin kasar inda a baya-bayan nan wasu mahara suka far wa yankin jihar Neja suka kashe wasu mutane.
A ranar jajiberin zaben Shugaban kasa a Amurka masana harkokin siyasa a Nigeria sun ci gaba da yin sharhi kan babban zaben da za a yi ranar Talata 3 ga watan Nuwamba.
Domin Kari